1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:Takun saka kan gyaran kundin tsarin mulki

December 20, 2017

Gwamnoni sun gudanar da taro da shugabannin majalisun dokoki na jihohi kan batun gyara ga kundin tsarin mulkin kasa inda gwamnonin ke zargin majalisun tarayya da kokarin hada kai da na jihohi wajen musu yankar baya.

https://p.dw.com/p/2phVn
Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Kama daga 'yanci na cin gashin kai a mataki na kananan hukumomi a Najeriya ya zuwa tabbatar da 'yan sanda na jihohi da ma uwa uba sa ke tsarin dimokradiya da rabon kudin tsarin mulki ya sa aka dauki lokaci game da bukatar sauyin fasalin lamura a kasar. Sai dai ana shirin fuskantar rikici sakamakon matakin majalisun tarayyar biyu na tsallake gwamnoni na jihohi tare da mika bukatar gyaran ga  majalisun jihohi na kasar kai tsaye.

Batun ya harzuka gwamnonin kasar da suke karatun yankan baya a bangaren 'yan dokan da ke neman 'yanci iri-iri amma kuma ke tsoron zartarwa. Kokari na gyara na kasa ko kuma cika burin son ran dai ga 'yan majalisun dokokin na zama babbar dama ta sauyi na rawa a bangaren 'yan dokar da suka dauki lokaci suna ji a jiki a cewar Yusuf Abdullahi  Atta shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano a arewacin kasar. Yanzu haka dai an zuba ido wajen ganin tasirin da muhawarar da ke dada kamari  cikin kasar mai shirin gudanar da zabe nan ba da jimawa ba.