1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tankiya kan albashin ma'aikata

October 18, 2017

Duk da kudade da jihohin, ciki har da Adamawan Najeriya suka karba daga gwamnatin tarayya, an shiga jayayya tsakanin gwamnatin Buhari da ta jihohin saboda kin biyan ma'aikata.

https://p.dw.com/p/2m79t
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Basukan albashin da ma'aikata ke bi a wasu jihohi a Najeriya, ciki har da Adamawa, na ci gaba da daukar hankali, duk da kudaden da jihar ta karba na Paris Club har sau biyu daga gwamnatin tarayya don ta biya albashin ma'aikatan.

Masu lura da al'amura da kaje su komo, na ganin kememen biyan albashin ma'aikatan da gwamnatocin jihohin ke yi ka iya shafar bangaren da abin ya shafa, abin da kuma zai iya gangarowa ya yiwa al'umma illa.

Daya daga cikin matsalolin da gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta daukarwa matakan gaggawa don samun mafita, ita ce matsalar basukan albashi da ma'aikata ke bin gwamnatocin jihohinsu. Abin da gwamnatin tarayyar ta yi shi ne bawa gwamnatocin jihohin kudaden ceto, don tallafa musu su iya biyan basukan albashin ma'akatan.

Polio Nigeria
Ma'aikatan lafiya ma kan ga tasku kan albashiHoto: AFP/Getty Images

Ana haka, sai batun salalar kudaden Paris Kulob ta bullo, inda jihohin suka karbi makudan kudade, wajen karo biyu, da zummar biyan albashi da fansho da garatuti. Amma abin mamaki da takaicin, duk da wadancan kudade da jihohin, ciki har da Adamawa suka karba, har yanzu wani rukunin ma'aikata a jihar na bin gwamnatin bashin watanni dai dai har biyar.

Wannan ta sa kungiyar ma'aikatan kiwon lafiyar sukai barazanar ajiye aiki nan da mako guda idan ba biya su bashin albashin da suke bin gwamnati ba, kamar yadda shugaba kungiyar Kwamared Jermiah Ngyarkwar ya fada.