1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yajin aikin malaman jami'a

August 15, 2017

Kungiyar Malaman jami’oi ta shiga yajin aikin gama gari a kasar bisa abin da ta kira gazawar gwamnati na cika yarjejeniyar da suka cimmawa.

https://p.dw.com/p/2iH7c
Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Hoto: DW/N. S. Zango

Daukan wannan mataki na yajin aiki da ya biyo kwashe kwanaki biyu suna gudanar da taro a Abuja cibiyar kungiyar ya sanya kungiyar malaman jami'on Najeriyar daukan wannan mataki wanda ya hada da kin cika alkawarin da suka cimawa da gwamnati a 2013 na sanya Naira triliyan 1.3 a cikin shekaru shida wanda sau daya gwamnatin ta bayar da Naira bilyan 200. Sannan ga batun kin biyansu sauran hakokinsu na Naira bilyan 30 baya ga batun kudadden fansho da suke fuskantar gibi na biyansu abin da ke shafan daukacin tsarin. Biodun Ogunyemi shi ne shugaban kungiyar ta ASUU.

Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Hoto: DW/N. S. Zango

'' Bisa ga tuntubar juna da membobinmu da taron majalisar zartaswa da muka yi a ranar Asabar 12 ga watan nan mun amince da kudurin mu shiga yajin aiki na sai baba ta gani daga ranar Lahadi 13 ga watan nan. Wannan yaji aiki na gaba daya ne don haka a lokacinsa babu koyar da dalibai ba jarawa ba wani taro kowane iri ne.''

Al'ummar Najeriya musamman dalibai da iyayensu na koke a kan yawaitar yajin aiki da malaman jami'oin ke yi abin da ke shafar tsarin karatu. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta fito ba ta yi magana dangane da yajin aikin wanda bisa ga dukkan alamu ke yin barazana ga sha'anin ilimi a Najeriyar.