1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zargin cusa wa matasa tsaurin kishin addini

Ubale Musa/ASJune 17, 2016

Hukumomi a Najeriya sun zargi kungiyar nan ta IS da yunkuri na cusa wa matasa akidar tsaurin kishin addini ta hanyar amfani da wata manhaja ta waya mai suna Huruf.

https://p.dw.com/p/1J8xQ
Syrien IS-Kämpfer
Hoto: picture-alliance/Balkis Press

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce IS na kokarin cusa akida a tsakanin matasa da wata sabuwar kafar koya karatun addini. Wata sanarwar ma'aikatar labaran kasar dai ta ce sabuwar manhajar mai suna na Huruf na dauke da hotuna na makamai da kungiyar ke amfani da ita da sunan koyon Larabci amma kuma ta na cusa akida ta jihadi. Wannan ne ma ya sanya ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed jan kunnen iyayen yara dangane da wannan batu.

Tuni dai al'ummar kasar da kuma masa harkokin tsaro da zamantakewa suka fara yin tsokaci kan wannan batu. Kabiru Adamu da ke sharhi kan lamura na tsaro a Najeriya din ya ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na jan kunnen mutane kan wannan sabuwar hanya ta cusa tsaurin kishin addini na ya yi daidai. Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da irin halin da kasar ta tsinci kanta a ciki ba na hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi irinsu Boko Haram da suke da alaka da kungiyar IS.

Boko-Haram-Chef Abubakar Shekau BITTE BESCHREIBUNG BEACHTEN / SCHLECHTE QUALITÄT
Wannan matsala na tasowa ne daidai lokacin da Najeriya ke kokarin kawo karshen hare-haren Boko HaramHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma in har jan kunnen na iya tasiri ga kasar da ke neman girgije tasirin kungiyar Boko Haram, daga dukkan alamu mahukuntan na Abuja na da dogon zango a kokari na burge iyayen kasar da tuni wasu ke musu kallo na siyasar ta ta'adda. Mallam Hussaini Zakariya wanda malamin addini ne a Abuja ya ce a ganinsa akwai banbanci a tsakanin kokari na kai karshe na ta'adda da kuma farfagandar neman burge turawa. Yanzu haka dai 'yan kasar sun zuba idanu don ganin yadda hukumomi za su kawar da wannan kalubale kafin waje ya kure musu.