1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nakiyoyi biyu sun sake fashewa a ƙasar Thailand

March 25, 2010

Nakiyoyi biyun da suka fashe a Thailand, sun lalata gine-ginen gwamnati a yayin zanga-zangar 'yan adawa

https://p.dw.com/p/Mbnx
Jami'an tsaron Thailand sun ja da'ga da masu zanga-zangar adawa da gwamnatiHoto: AP

Hukumomin ƙasar Thailand sun bayyana cewar, zasu ƙara tsaurara tsaro bayan da wasu abubuwa biyun da suka ƙara fashewa sun lalata wasu gine-ginen gwamnati, wanda kuma shine na baya bayannan cikin jerin abubuwan dake fashewa tun sa'adda masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin ƙasar suka fara yin jerin gwanonsu a 'yan kwanakinnan. Gangamin, wanda magoya bayan tsohon Frime Ministan ƙasar Thaksin Shinawatra suka ƙaddamar, ya sanya gwamnati tura ƙarin jami'an tsaro, ciki kuwa harda fito na fito a majalisar dokokin ƙasar, wanda ya janyo 'yan adawa suka ƙauracewa zaman majalisar. Hukumomin suka ce, fashewar sanadaran, ta lalata wani babban ɗakin taro na gwamnati, da kuma wasu gine-ginenta inda kimanin mutane 5,000 ke yin aiki.

Muƙaddashin Frime Ministan Thailand Suthep Thaugsuband, ya shaidawa manema labarai cewar, tuni ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro domin - a cewarsa, wasu rahotanni daga jami'an leƙen asiri na nuni da cewar, masu zanga-zangar na son tada zaune tsaye ne, ta yadda za'a ga kamar gwamnati ta gaza tafiyar da mulki ne, amma ya ce, yana bayar da tabbacin cewar, gwamnati nada cikakken iko tafiyar da harkokin mulki a ƙasar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas