1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NAMIBIA: SHUGABA NUJOMA YA YI MURABUS BAYAN SHEKARU 15 KAN MULKI.

YAHAYA AHMEDMarch 22, 2005

Shugaban Namibia, Sam Nujoma, ya mika ragamar mulkin kasar ga magajinsa, HIFIKEPUNYE POHAMBA, a ranar bikin cika shekaru 15 da samun `yancin kasar. Shi dai Nujoma, mai shekaru 75 da haihuwa, ya ce zai koma jami'a ne don ya yi karatu a fannin ilimin sanin ma'adinai. Kazalika kuma, zai ci gaba da rike shugabancin jam'iyyar da ke mulki a kasar a halin yanzu, wato SWAPO.

https://p.dw.com/p/Bvch
Tsohon shugaban kasar Namibia, Sam Nujoma, wanda ya yi murabus, bayan shekaru 15 kan mulki.
Tsohon shugaban kasar Namibia, Sam Nujoma, wanda ya yi murabus, bayan shekaru 15 kan mulki.Hoto: AP

Sam Nujoma dai ya bar tarihi a kasar Namibiya. A cikin rayuwarsa, ya shafe shekaru 25 yana yakin sunkuru don nemar wa kasarsa `yanci. Bayan samun `yancin ne kuma ya zamo shugaban kasar Namibiya, a cikin shekarar 1990. A ran 21ga watan Maris, ranar bikin cika shekaru 15 da samun `yancin kasar, da kuma kasancewarsa kan karagar mulki ne, Sam Nujoma ya mika wannan mukamin ga dan hannun damansa, kuma abokin gwagwarmayarsa a yakin neman `yanci, Hifikepunye Pohamba. Ban da rike mukamin shugaban jam’iyyar SWAPO da ke jan ragamar mulki a kasar da zai ci gaba da yi, Sam Nujoma, wanda a halin yanzu ke da shekaru 75 da haihuwa, ya kuma bayyana cewa, zai fara karatu a fannin ilimin sanin ma’adinai, wato Geology a turance, a jami’ar Namibiya da ke birnin Windhoek.

Manazarta harkokin yau da kullum a nahiyar Afirka dai, sun nuna mamakinsu ga yadda Sam Nujoma ya sauka daga mukaminsa cikin lumana. Kamar yadda wani shaihin malami a fannin shari’a na jami’ar Namibiya, Manfred Hinz ya bayyanar:-

"Jama’a da yawa sun yi wa Nujoma kallon wani sarki ne na gargajiya, mai cikakken iko, wanda kuma zai ci gaba da rike wannan mukamin ne har karshen numfashinsa. Amma sai ga shi hakan bai auku ba. Wannan sauka da ya yi da kansa daga mukaminsa, ba a ko’ina ake samun irin haka a nahiyar Afirka ba."

Har ila yau dai Sam Nujoma na da kwarjini a bainar jama’ar kasar ta Namibiya. Sai dai manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, a duk tsawon lokacin mulkinsa, bai iya ya cika alkawarin rage gibin da ke tsakanin bakake da fararen fatan kasar ba. A ganin Matthias Basedau, na cibiyar nazari kan nahiyar Afirka da ke birnin Hamburg a nan Jamus:-

"Babban gibin da ake da shi a fannin tattalin arziki, tsakanin bakake da fararen fatan kasar a lokacin samun `yanci, har ilya yau bai ragu ba, shekaru 15 bayan samun `yancin kasar. Jam’iyyar SWAPOn da sabon shugaba Pohamba dai, ba za su iya ci gaba da dogaro kawai kan nasarar da suka samu wajen yakan Afirka Ta Kudu da manufofinta na wariyar al’umma a lokacin yakin neman `yanci ba."

Babu shakka, sabon shugaba Pohamba dai, yana cikin masu kambama wannan zamani na yakin neman `yanci. Sai dai, matasan kasar na yanzu, ba su da wata jibinta sosai da wannan fafututkar da magabatansu suka yi. Da yawa daga cikinsu na yara kanana, lokacin da kasar ta sami `yanci. Sabili da haka, labarin gwagwarmayar da aka yi, a lokacin yakin neman `yanci ma, suna daukarsa ne kamar tatsuniya. A bangare daya kuma, kara samun yawan marasa aikin yi tsakanin matasan, wani abin damuwa ne ga mahukuntan kasar. A halin yanzu dai, kusan kashi 30 cikin dari, na matasa bakaken fata ne ba su da aikin yi a kasar. Kamar yadda Matthias Basedau ya bayyanar:-"Kawo yanzu dai, gwamnatin Namibiya ta fi mai da hanakli ne wajen bai wa matasan horo – ta hanyar zurfafa iliminsu ko kuma koyon sana’o’i. Amma duk wadannan matakan, na lokuta ne masu tsawo. Sabili da haka ne, ake ta samun hauhawar tsamari a bainar jama’a wadanda ba su da dauriyar jira har zuwa lokacin girbi."

Fararen fatan kasar da kuma kasashen Yamma na fargabar cewa, matsalar za ta iya tabarbarewa, idan ba a samo bakin zaren warwareta ba. Mai yiwuwa don kwantar wa al’umma hankali, jam’iyyar SWAPOn ta shiga aiwatad da kudurorin yi wa mallakar filaye garambawul a kasar, kamar dai yadda aka samu a kasar Zimbabwe. Tun shekaru 15 da suka wuce, wato a lokacin samun `yanci ne, gwamnatin Namibiyan ta yi ta alkawarin sake rarraba filayen noma na kasar bisa adalci. Amma har ila yau, fararen fatan ne ke rike da mafi yawan filayen masu albarka.

Duk da hakan dai, manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, ba za a shiga wani yanayi a kasar irin na Zimbabwe ba. Shaihin malami Manfred Hinz shi ma ya goyi bayan wannan ra'ayin. Ya dai kara bayyana cewa:-

"Abin farin ciki ne, lura da yadda aka sami ci gaba iya gwargwado, cikin shekaru 15 da suka wuce. Idan dai aka kwatanta Namibiya da wasu kasashen Afirka da dama da irin matsalolin da suke huskanta, za a gani a zahiri cewa, a nan kasar ana tafiyad da doka da oda, kotunanmu kuma na aiki iya gwargwado. Ana kuma samun gagarumin ci gaba a fannin ilimi. Duk wadannan, wato nasarori ne da aka cim ma, tun lokacin samun `yanci, kuma ana iya ganin sakamakon da suka haifar a ko’ina."