1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kewayowar ranar kawo karshen mulkin mallakar Jamus

Yusuf BalaJuly 9, 2015

Rana mai kamar ta yau tara ga watan Yuli, ita ke tunawa al'ummar kasar Namibiya shekaru dari da kawo karshen mulkin mulaka'un kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/1Fvab
Deutsches Reich Kolonialgeschichte Genozid an den Hereros
Hoto: public domain

Wata gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu shida na nan Jamus tare da wata 'yar siyasar kasar Namibiya sun gabatar da korafi ga shugaban kasar Jamus Johannes Gauck cewa, kasar ta dauki alhakin kisan kiyashi da ya faru a farkon karni na ashirin a wannan kasa da suka yi wa mulkin mallaka.

A ranar Litinin 'yar majalisa daga kasar Namibiya Ida Hoffmann ta yi kokarin gabatar da korafi ga shugaban kasar Jamus Johannes Gauck domin kasarsa ta dauki alhakin kisan kiyashi da ak yi wa al'ummar kasarta.

Sai dai me ya faru? Ga abin da 'yar majalisa Hofmann ke cewa:

"Amma abin takaici shugaban bai fito ba".

Matakin da Ida Hoffmann ta bayyana da cewa cin fuska ba wai ga kasar ta Namibiya ba har ma ga 'yan kasar ta Jamus.

Deutschland Namibia Schädelübergabe
Ida HoffmannHoto: Scholz/DW

Ta ce: mutane da dama a nan Jamus sun amince da rattaba kan wannan korafi, mun gode musu, dan haka ne muka zo nan Jamus sai dai babu abin da muka gani sai rashin mutuntawa.

'Yar majlisa Hoffmannn dai tare da wadannan kungiyoyi masu zaman kansu na bukata ne Jamus ta nemi afuwa kan kisan kiyashi da aka yi wa al'ummar Nama da Herero.

Jamus ta taba yin mulkin mallaka a abin da ake kira Namibiya a yau da suka kira Kudu maso Yammacin Afrika. A tsakanin shekarun 1904 zuwa 1908 lokacin mulkin mallakar ta Jamus mutane dubu tamanin ne aka kashe a wani kisan kare dangi bisa sa hannun masarautar Sarki Wilhelm na biyu na Jamus, aka kuma aiwatar karkashin umarnin Janar Lother von Trotta. A wancan lokaci kashi 80 cikin dari na al'ummar Herero da kashi 50 cikin dari na al'ummar Nama an aikasu lahira.

Ko da yake an dade da mantawa da wannan labari a Jamus amma al'ummar ta Namibiya tun daga shekarar 1932 sun rika ware wannan rana dan tunawa da mutanensu. A bangaren na gwamnatin ta Jamus ta yi gum da bakinta sai a shekarar 2004 lokacin da ministar raya kasa a Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul ta kai wata ziyara Namibiya ta nemi afuwa:

Ta ce : A yau zan bayyana amincewarmu da kisan kare dangi da aka aikata wa kakaninku karkashin Jamusawa da suka yi muku mulkin mallaka musamman 'yan kabilar Herero da Nama., irin cin zarafi da gallazawa da kisan gilla da aka yi a wancan lokaci shi ake kira kisan kare dangi.Janar Lothar von Trotta za a gurfanar da shi a caje shi. Cikin kalaman mahillici cikin addu'a na nemi ku yi mana afuwa kan take hakkinku da abin da muka aikata"

Demonstration bei der Rückgabe von Hererogebeinen
Hoto: AFROTAK TV/Michael Kueppers-Adebisi

Wannan dai ba karamin koma baya bane a fafutikar da kungiyoyi masu zaman kansu na Jamus ke yi a nemin afuwar cikin bukatunsu guda hudu a cewar Christian Kopp na Berlin Postcolonial.

Ya ce : Na farko su amince an aikata kisan kiyashi a nemi afuwa daga mataki mafi kololuwa a kasar kamar ofishin shugabar gwamnati ko mataimakinta ko majalisa, a maida ragowar gawarwakin da aka kawo Jamus, sannan gwamnati ta daidaita kai tsaye da 'yan Nama da Herero.

Babban abin da ke zama kadangaren bakin tulu a rikicin na zama yadda har yanzu akwai dubban kasusuwa na wadannan al'umma da ke watse a dakunan bincike a nan Jamus wanda 'yar majalisa Hoffmann da sauran kungiyoyi masu zaman kansu na nan Jamus ke son gani an maida su Namibiya, kuma suna kallon yadda Jamus ta amince da Turkiya ta yi kisan kiyashi kan Armaniyawa amma ta nemi kaucewa kan laifin da ta aikata.

Hoffman dai ta nufi birnin Landan dan neman kwararrum lauyoyi da suka tsaya kan shari'ar Kenya da Birtaniya a gallazawar da al'ummarta suka fuskanta a shekarun 1950.