1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar Kungiyar Hamas a zaben Falasdinu.

January 27, 2006

Sakamakon zaben da aka gudanar a yankunan Falasdinawa dai na nuna cewa, kungiyar Hamas ce ta ci nasara. To ko wane irin sauyi wannan nasarar ta Hamas za ta iya janyowa a fagen siyasar yankin gaba daya ?

https://p.dw.com/p/Bu24
Babban dan takarar Kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh.
Babban dan takarar Kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh.Hoto: AP

Kalmar Hamas dai, sunan kungiyar nan “Harakat Al-Muqawama Al-Islamia” ne a takaice, wato kungiyar daddagewa ta islama. Tun shekarar 1987 ne dai ta bayyana a zirin Gaza da kuma Gabar Yamma, tamkar kungiyar isalama mai neman komawa ga addini na tsantsa, wadda ke kalubalantar kungiyar PLO ta Yasser Arafat. Sabili da wannan matsayin da Hamas din ta dauka ne Gwamnatin Isra’ila ta mara mata baya, don dai gindaya wa PLO din shinge a fafutukar da take yi ta kawsancewa ita kadai ce ke wakilcin duk al’umman Falasdinu. Ita dai Isra’ilan ta yi hakan ne don ta nuna wa duniya cewa, a yankunan da ta mamaye ma, akwai rukunai da ke wakilcin Falasdinawan, wadanda kuma suka fi PLO din angizo a yankunan. A wannan lokacin mahukuntan Isra’ilan a birnin kudus na kyautata zaton cewa, kungiyar addini kamar Hamas wadda ta dukufa wajen ba da taimakon agaji ga Falasdinawa, ita ce za ta iya maye gurbin rikakken abokin gabanta, wato Yasser Arafat.

Kafin ma daure wa Hamas din gindi dai, sai da Isra’ilan ta yi kokarin kikiro waso rukunan Falasdinawa `yan amshin shatanta a kauyukan yankin Gabar Yamma da kuma Zirin Gaza, amma ba tare da cin nasara ba.

Ita dai Hamas ta yi tashe ne a cikin shekarar 1987, yayin da Falasdinawa suka fara farkon borensu na Intifada. A nan ne ta fito fili ta yi kira ga daddage wa Isra’ila, inda ta bukaci Falasdinawa su yi yajin aiki, sa’annan kuma ta angaza mayakanta su yi ta kai wa Isra’ilan hare-hare. Ta yin kwaikwayo dai da manufofin kungiyar nan ta Muslim Brotherhood ta kasar Masar, Hamas, ta lashi takobin nuna matukar adawa ga Isra’ila inda ta ce burinta ne daddage wa Hukumar mamaye ta kasar bani Yahudun, ba ma a yankunan da ta mamaye kawai ba, har ma cikin kasar Isra’ilan da kanta.

To har ya zuwa yanzu dai, Hamas ba ta kaucwe daga wannan akidar ba.

A lokacin da Isra’ila ta kulla yarjejeniyar Oslo da kungiyar PLO a shekarar 1993 a kasar Norway, kungiyar Hamas din ce ta farko da ta yi Allah wadai da yarjejeniyar, inda ta ce wato PLO ta sayad da duk al’umman Falasdinawa ne da sanya hannu kan wannan takardar. A lokacin da za a gudanad da farkon zaben Falasdinawa a shekarar 1996 kuma, Hamas kaurace wa shirin ma ta yi gaba daya, ta ki shiga zaben. Sannu a hankali dai, sai kungiyar ta yi ta samun angizo a yankunan Falasdinawan. Hare-haren da mayakanta da kuma na kungiyar nan ta Islamic Jihad suka yi ta kaiwa a Isra’ilan a cikin shekarar 1996 ne dai suka taimaka wajen samun nasaran Benjamin Netanyahu, a zaben da aka gudanar a Isra’ilan, don samad da wanda zai gaji Firamiyan kasar Yitzhak Rabin da aka yi wa kisan gilla. Shi dai Netanyahu, da ma can rikakken mai adawa ne da yarjejeniyar ta Oslo. Sabili da haka ne kuwa, da hawansa kan karagar mulki, ya yi duk iyakacin kokarinsa wajen ganin cewa, kome ya cije a shawarwarin ci gaba da aiwatad da ka’idojin yarjejeniyar.

A yankunan Falasdinawan dai a halin yanzu, kungiyar ta Hamas na gudanmad da ayyukan ba da taimakon agaji ne ga jama’a, musamman ma dai talakawa da kuma marasa galihu.

Sai dai, a huskar siyasa, ba ta ja da baya ba daga akidarta ta kin amincewa da wanzuwar Isra’ila tamkar kasa. Bugu da kari kuma, tana da kyakyawar hulda da Siriya da kuma Iran, wato kasashen da su ma ke matukar gaba da Isra’ilan. A kwanakin bayan ne ma shugaban kungiyar ta Hamas, da ke zaman gudun hijira a birnin Damascus, Khaled Mashal, ya ziyarci shugaba Mahmood Ahmadinijad na kasar Iran a birnin Teheran. Yayin da shugaban na Iran ya kawo ziyara a Siriya kuma, sai da suka sake saduwa da juna a birnin na Damascus.