1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar yarjejeniyar hana kera nakiyoyin karkashin kasa.

Mohammad Nasiru AwalFebruary 27, 2004
https://p.dw.com/p/Bvld
A halin da ake ciki yarjejeniyar kasa da kasa wacce ta haramta amfani da ko-wace irin nakiya ta karkashin kasa, ta fara yin tasiri. Masu kera irin wadannan makamai da kasashen dake amfani da su, sun samu kansu cikin wani mawuyacin hali sakamakon wannan yarjejeniyar, inji Andreas Rister na kungiyar ba da agaji ta terre des hommes.

"Yanzu dai muna cikin wani hali, inda ake samun raguwar amfani da nakiyoyin karkashin kasa. Haka nan cinikin wadannan makaman ya ragu matuka ainun. Yanzu haka dai an lalata nakiyoyin karkashin kasa kimanin miliyan 50 a karkashin yarjejeniyar ta Ottawa. To sai dai kusan an gudu amma ba´a tsira ba, domin har yanzu kasashe masu arzkiin masana´antu na ci-gaba da kera irin wadannan makaman."

Saboda haka ake samun koma-baya dangane da nasarar da wannan yarjejeniya ta samu yau shekaru biyar bayan an sanya mata hannu. Domin duk da cewa kasashe 150 sun sanya hannu akan yarjejeniyar, amma har yanzu manyan kasashe da suka fi kera nakiyoyin karkashin kasa kamar Amirka da Rasha da China da Indiya da kuma Pakistan ba su rattaba mata hannu ba. Alkalumman da aka bayar sun yi nuni da cewa akwai irin wadannan makaman kimanin miliyan 300 a duniya yayin da kimanin miliyan 100 kuma ke binne a karkashin kasa. Duk da wannan yarjejeniyar kuwa akwai irin wadannan nakiyoyin bibbine a yankunan da ake fama da rikici kamar Angola, Afghanistan da kuma Kososvo, yayin da mutane sama da dubu 100 suka mutu ko suka samu raunuka sakamakon nakiyoyin karkashin kasa, inji kungiyar ba da agaji ta terre des hommes.

An jiyo Vera Bohle, daya daga cikin Jamusawa dake aikin tone nakiyoyin karkashin kasa na bayannan aikin da suke yin da cewa mai hadarin gaske ne duk da sabbin kayan aikin da ake da su yanzu.

Shi kuwa Andreas Rister cewa yayi babban kuskure ne da yarjejeniyar ta Ottawa ba ta haramta kera dukkan nakiyoyin da ake da su a duniya ba, musamman manyan nakiyoyi masu karfi, wadanda ke iya tarwatsa motocin yaki ko motocin fasinja.

Daukacin irin wadannan nakiyoyin kuwa ka iya fashewa da zarar wani abu komin rashin nauyin sa ya hau kan su. Bisa alkalumman da kungiyar ba da agajin ta bayar, rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr na mallkar irin wadannan nakiyoyi da yawansu ya kai miliyan 1.4. Ko da yake tun a shekarar 1997 gwamnatin tarayyar Jamus ta daina taimakawa aikin kera nakiyoyi, amma kamfanonin kasar na ba da gudummawa wajen kera irin wadannan makaman a duniya.