1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190508 Integrative Kindergärten

Yordanova, Yordanka May 27, 2008

Haɗe yara naƙasassu da sauran yara a makarantun nasare

https://p.dw.com/p/E7DL
Kula da yara naƙasassuHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Mu Kewaya Turai, shiri da kawo muku batutuan da suka shafi Turai da kuma dangantaka tsakanin ƙasashen wannan nahiya.


A kullum ji ake yi cewa babban burin da aka sa gaba shi ne shigar da mutane masu naƙasa cikin rayuwa ta yau da kullum. To amma kowa na da irin ma´anar da yake ba wannan kalma. A ƙasashe da dama nesanta kai daga mutane masu naƙasa ba baƙon abu ba ne. Ga iyayen yara naƙasassu kuwa samarwa ´ya´yansu wurare a nasare abu ne mai wuyan gaske. Sau da yawa ana tura su makarantu na musamman da aka tanadarwa yara naƙasassu. Don tinkarar wannan matsala a nan Jamus an fara gina makarantun ƙananan yara na kowa da kowa. Shin yaya irin waɗannan makarantun ke aiki kuma mene ne musamman a cikinsu? In kun biyo mu a hankali zaku ji cikakken bayani a cikin shirin wanda ni MNA zan gabata.


Allah ɗaya gari bambam. Wannan dai shi ne manufar kafa nasare ta kawo da kawo. Tun a cikin shekarun 1980 aka fara gwajin irin waɗannan makarantun a nan Jamus. Akwai na hukuma da kuma na masu zaman kansu waɗanda ƙungiyoyin iyaye kamar wata ƙungiya da ake kira Action Rainbow dake nan Bonn ke kafawa. Tun kimanin shekaru 14 da suka wuce Carmen Heinemann ke shugabantar wannan ƙungiya.


1. "A shekara ta 1983 muka kafa ƙungiyar don tinkarar matsalar ƙarancin wurare a nasare ga yara naƙasassu a birnin Bonn. Iyayen yara suka kafa wannan ƙungiya."


Hukumar jihar North Rhein Westaflia da ofishin kula da matasa na birnin Bonn ke ɗaukar nauyin tafiyar da wannan shiri. Yayin da su kuma ƙungiyar iyaye ke taimakawa da kimanin kashi biyu cikin 100. Su kuma iyayen yara suna ba da gudunmawar kuɗi da ta dogara ga yawan albashinsu, inji Carmen Heinemann sannan ta ci gaba da cewa.


2. "Wannan wani gagarumin mataki ne da iyayen suka ɗauka. Suna ba da ta su gudunmawa iya gwargwado. Suna taimakawa wajen tsabatace makarantun da harabobinsu. Saboda haka ba sai mun ɗauki wani yayi mana wannan aiki ba."


Tsarin aiki da koyarwa a makarantar yara ta Action Rainbow na gudana ne bisa wani tsarin renon yara da wata likita ´yar Italiya mai suna Maria Montessori ta shirya a farkon ƙarni na 20. Wannan tsari yana ba wa yaran damar tinkarar duk wani ci-gaba ko sauyi da zai dace da buƙatunsu na rayuwa. Yaran dai na iya shiryawa kansu wasu abubuwa daidai da yadda ƙarfinsu ya ke. Yayin da wakilan ƙungiyar da kuma iyaye suke aiwatar da wannan tsari na reno.


A nasaren dai akwai rukunan yara guda biyu. Kowane rukuni na ƙunshe da yara 15 masu naƙasa iri daban daban. Ta haka suna cin amfanin juna inji Carmen Heinemann.


3. "Suna aiki tare da girmama juna. Idan yaro na da wata naƙasa ba ya nufin ya na naƙasa ko wani koma baya kenan a dukkan ɓangarorinsa na rayuwa. Yaran na ganewa idonsu cewa yaron da ba ya iya tashi ko tafiya ba wai ya naƙasu a dukkan gaɓoɓinsa ne ba, a´a shi ma wataƙila yana da wata hazaƙa da Allah Ya ba shi."


Babban burin ma´aikatan makarantun yara na kowa da kowa kamar yadda Carmen Heinemann ta yi bayani shi ne ilimantar da yara muhimman fannoni na rayuwa wato kamar haƙuri da juriya da girmama juna ba tare da nuna wariya ba. Ta ce waɗannan su ne abubuwa da suka fi bawa muhimmanci. Kuma yana taimakawa yaran wajen tinkarar ƙalubalen rayuwarsu ta yau da kullum. Ita kuwa Christiane Dahl wadda ta tura ´ya´yan uku zuwa makarantar nasaren dake ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Action Rainbow ta yi fatan cewa sauran iyaye ma za su riƙa tura ´ya´yansu irin wannan makarantu don koyan darasi na rayuwa.


5. "Yara na koyan darussa na rayuwa a cikin ire-iren waɗannan makarantun nasare wato kamar yadda za a shigar da masu rauni a cikin jama´a. Amma gaskiya ko koɗan ba na son yin amfani da kalmar masu rauni sai dai ce mutanen da aka halicce su daban. Abin sha´awa ne yadda suke da hazaƙar da kuma saurin gane abubuwa."


Cibiyar ta shigar da yara daban daban na da fa´idoji masu yawa ga yara naƙasassu. Abubuwa da ake nuna musu na da nasaba da rayuwar yau da kullum. Ba wai a azuzuwa ne kaɗai malaman ke kula da yaran ba, a´a ana kuma duba matsalolin su da sauran ƙalubale na rayuwa da suke cin karo da su. Veronika Heilbing ta zaɓarwa tagwayenta waɗanda dukkansu biyu ke da naƙasa, wannan nasare ta ƙungiyar Action Rainbow.


6. "Akwai dalilan zaɓarwa yara wannan nasare musamman idan sun kasance naƙasassu. Wani dalilin shi ne na kula da lafiyarsu, inda ake ba da shawarar da ka da mu tura yara zuwa nasare ta naƙasassu sai ta kowa da kowa, domin a nan sun fi samun taimako da kulawa mafi dacewa da irin halin da suke ciki. Suna kuma samun damar yin cuɗanya da sauran yaran da ke da naƙasa irin ta su da kuma waɗanda ba su da wani rauni kuma suke yin komai ba da wani tarnaƙi ba. Ɗaya dalili kuma na da nasaba da siyasa. Bambamta makarantu ba abu ne da na ke gani ya dace ba. Saboda haka ko da yara na ba su da wata naƙasa da ba zan tura su wata makaranta ta daban ba."


Duk da cewa ana maraba da irin wannan nasare ta kowa da kowa a nan Jamus amma duk da haka yaran nasaren ta Action Rainbow na fama da wasu matsalolin, inji Christiane Dahl.


7. "Akwai wasu abubuwan da suka zama dole yaran da ma iyayae su ba da la´akari kansu. Alal misali wajen yin balaguro musamman a wajen gari, domin ba dukkan yaran ne ke iya yi ba saboda rauni da suke da shi na tafiya. Saboda haka dole ake taƙaita yin irin waɗannan tafiye-tafiyen. Wannan dai wani koma baya ne amma ba ya zai sa mu yi ƙasa a guiwa ba."


Ko da yake akwai kyawanan tsare tsare na makarantu nasare na kowa da kowa a nan Jamus kuma suna aiki. Suna zaman wata aljanna idan aka kwatanta da abin da ke zuwa baya, wato rashin irin wannan tanadi a makarantun firamare, inda a dole ake raba su da sauran yara da kuma abokane da suka saba da su a lokacin nasare.