1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO da harkokin tsaro a ƙasar Afghanistan

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujd

Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya kaɗa ƙuriár amincewa da faɗaɗa hurumin zaman dakarun NATO a ƙasar Afghanistan tare da baiyana damuwa ga ƙaruwar tarzoma da ayyukan taáddanci na ƙungiyar Taliban da al-Qaída da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi a Afghanistan. Dakarun sojin na NATO na fuskantar matsanancin martani daga yan Taliban waɗanda ke yin barazana ga shaánin tsaro a ƙasar Afghanistan.

Wakilan ƙasashen ƙungiyar tsaron ta NATO za su gudanar da taro domin duba yiwuwar ƙara yawan dakarun sojin domin tunkarar boren na yan Taliban. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta ɗaukaka kira ga ƙungiyar NATO cewa kada ta ƙosa da a yayin da ƙasar ta Afghanistan take ƙoƙari domin kafa ƙwaƙwarar dimokraɗiya mai ɗorewa. Tana mai kashedi da cewa yin watsi da ƙasar zai iya haifar da mummunan sakamako. A farkon wannan makon sakataren ƙungiyar tsaron ta NATO Jaap de Hoop Scheffer ya buƙaci wakilan ƙasashe su bada ƙarin gudunmawar soji ga rundunar don tunkarar ƙalubalen da take fuskanta daga Taliban. A halin da ake ciki rundunar na da dakaru 20,000 waɗanda ke aikin tsaro a ƙasar Afghanistan. A waje guda kuma shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharraf ya baiyana yan Taliban da cewa sun fi haɗari fiye da ƙungiyar al-Qaída ta Osama bin Laden.