1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO da Rasha sun yi wa juna barazana

Gazali Abdou Tasawa
June 21, 2017

Wani jirgin yakin rundunar kawancen tsaro ta NATO ya  yi wa jirgin da ke dauke da ministan tsaron kasar Rasha Serguei Choigou barazana a wannan Laraba a saman tekun Baltika. 

https://p.dw.com/p/2f79C
Deutschland Tornado Flugzeug Luftwaffe Symbolbild Syrien-Einsatz Bundeswehr
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Wani jirgin yakin rundunar kawancen tsaro ta NATO ya yi wa jirgin da ke dauke da ministan tsaron kasar Rasha Serguei Choigou barazana a wannan Laraba a saman tekun Baltika. 

Wasu 'yan jaridar kasar ta Rasha da ke tare da tawagar ministan kasar ta Rasha a cikin jirgin saman lokacin da lamarin ya afku, sun ruwaito cewa jiragen yakin kungiyar ta NATO sun yi yunkurin yi wa jirgin ministan tsaron Rashar zagi har daya daga cikinsu ya kusanci shi fiye da kima, amma nan take wani jirgin yakin kasar ta Rasha da ke yi wa na ministan tsaron rakiya ya tilasta wa jirgin yakin Kungiyar ta NATO mazayawa, da ma nisantar jirgin ministan, bayan da ya nuna mashi cewa yana dauke da makami kuma a shirye yake ya yi amfani da shi a kan shi. 

Wannan sabon hadari dai na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin kasar ta Rasha da kasashen Kungiyar ta NATO musamman kasar Amirka a yankin Gabashin Turai.