1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta kara waadinta a Darfur

April 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0m

Kungiyar kawance ta NATO,ta kara waadin aiyukanta na horasda dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur,har sai watan satumba mai zuwa,amma tace bata shirin kara yawan dakarunta zuwa yankin na Sudan da yaki ya tagaiyara.

Komanadan rundunonin NATO a darfur,janar James L Jones na Amurka,yace a karshen wannan wata ne tun farko aka shirya aiyukan dakarun na NATO zai kawo karshe,amma yanzu kasashe 25 na kungiyar sun amince da kara waadin ayiukan dakarun nasu,hakazalika yace,masana harkokin sohji sun fafa shirin sake horasda dakarun kungiyar AU su 7,000 tare da basu jirage da zasu rika dauko wasu dakarun na Afrika.