1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta karbi jagorancin dakaru a Afghanistan

October 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuhJ

Kungiyar tsaro ta NATO ta karbi ragamar jagorancin dakarun Amurka fiye da 12,000 a Afghanistan.

Tunda farko dai kasar Amurka ke jagorancin rundunonin.

Da karin sojojin na Amurka,yanzu haka sojin dake karkashin NATO a yankin yawansu ya kai 30,000.

Komandan rundunar ta NATO wajen bikin karbar sojin na Amurka Janar David Richards yace sojin na Amurka zasu taimakawa zasu kara karafa aiyukan rundunonin kasa da kasa dake yankin.

Yanzu haka akwai wasu karin dakaru 8,000 da aka girke a gabashin Afghanistan karkashin jagorancin Amurka.

Kasar Jamus ma tana da dakarunta 2,800 a kudancin kasar.