1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta maida martani game da aikewa da jamianta zuwa Darfur

Hauwa Abubakar AjejeApril 11, 2006

Kungiyar tsaro ta Nato tace yan tsirarun jamianta take shirin aikawa zuwa Darfur,ba dakarun soji ba.

https://p.dw.com/p/Bu0i
Hoto: AP

Tun farko dai jaridar Washington Post ta Amurka ta bada rahoton cewa,kasar Amurka zata shawarta aikewa da daruruwan jamiai da zasu hade dana AU a yankin na Darfur.

Jaraidar tace gwamnatin Bush,tana bukatar wadannan jamiai su taimaka a fannonin sadarwa,leken asiri da sauran aiyuka na taimako ga dakarun na Kungiyar Taraiyar Afrika.

Rahotannin sunce,shirin zai hada da fiye da masu bada shawara ba kungiyar NATO 500 ciki har da wasu dakarun Amurka.

Jamian sojin NATO dai suna duba hanyoyin bunkasa aiyukan wanzar da zaman lafiya a Darfur,kamar yadda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan ya bukata.

Jamiai daga hedkwatar kungiyar sunce,Amurka zata yi kokarin neman kasashen kawance su aike da daruruwan sojojinsu zuwa Darfur,kodayake a nasu bangaren jamian NATO sunce suna duba yiwuwar aikewa da jamiansu kadan ne zuwa yankin.

Mai Magana da yawon kungiyar NATO,Carmen Romero,tace batun aikewa da sojojin NATO zuwa Darfur bata taso ba,tace abinda suke shirin yi shine aikewa sa jamian da zasu taimaka a fannoni da basu shafi na aikin soji ba.

Tuni dai NATO take da wasu jamianta a yankin na Darfur,wadda wasu daga cikinsu suke horasda dakarun kungiyar AU,da wasu aiyukan na dabam.

Dakarun na AU da yawansu ya kai 7,000 a yankin na Darfur,basu da isassun kayan aiki da zasu iya kawo karshen tashe tashen hankula da sukayi sanadiyar rayukan daruruwan mutane.

Kungiyar ta AU ta amince da aikewa da dakarun na MDD domin mara mata baya,sai dai gwamnatin Sudan tayi gargadin cewa,duk wata runduna da ta kuskura ta shiga yankin na darfur ba tare da amincewarta ba,to shfawa kanta ruwa,musamman ma dakarun da suka kunshi sojojin Amurka dana Kungiyar taraiyar Turai.

Kungiyar Taraiyar Afrika karkashin matsin lamba daga membobinta kasashen larabawa,wadanda mafi yawansu suke goyom bayan Sudan,tana dar dari da kwashe ya nata ya nata daga Darfur.

Shawarar aikewa da wadannan jamiai wani mataki ne na wucin gadi kafin aikawa da babbar runduna ta Majalisar Dinkin Duniya da zata dauki nauyin aiyukan wanzar da zaman lafiya a Darfur.

Tare da nufin kawo karshen kashe kashen gilla da fyade cikin yakin shekaru 3 tsakanin gwamnati day an tawaye,wanda ya tagaiyara kimanin mutane miliyan 2,ya kuma jefa yankin cikin halin kaka nikayi.