1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta yi gargaɗin taɓarɓarewar al’amura a Afghanistan.

October 9, 2006
https://p.dw.com/p/BugW

Babban kwamandan rundunar ƙungiyar ƙawance ta NATO a Afghanistan, Laftanan-Janar David Richards, ya yi gargaɗin cewa, idan ba a ɗau matakan inganta halin rayuwar jama’ar ƙasar ba, to za a sami haɓakar magoya bayan ƙungiyar Taliban. Ƙasar ta Afghanistan dai, inji kwamandan, na cikin wani hali ne na sauyi. Idan ko a cikin watanni 12 masu zuwa ba a sami wani ci gaba a yunƙurin inganta halin rayuwar jama’ar ƙasar ba, to da yawa daga cikinsu ne za su mai da alƙiblarsu wajen nuna cikakken goyon baya ga ƙungiyar Taliban.