1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari game da nasarar da kungiyyar Hamas ta samu

Ibrahim SaniJanuary 27, 2006

Nasarar jam´iyyar Hamas da alama na neman haifar da rudani a harkokin siyasarr yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/BvTw
Isma´il Haniyeh
Isma´il HaniyehHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai wannan gagarumin rinjaye da kungiyyar ta Hamas ta samu a zaben yan majalisun dokokin yankin da aka gudanar,na a matsayin wani babban kalubale ne ga mahukunta Amurka,musanmamma a kokarin da kasar keyi na wanzar da zaman lafiya a tsakanin yankin da Israela, a hannu daya kuma da wanzuwar mulki irin na dimokradiyya, a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

A misali a cewar wasu rahotanni daga Amurka, mahukuntan kasar sun kashe tsabar kudi har dala miliyan biyu a gudanar da aikace aikace a guraren da kungiyyar Hamas ta samu gagarumin rinjaye, a zabubbukan kana nan hukumomi da aka gudanar. Hakan a cewar bayanan anyi ne da nufin dago da darajar Jam´iyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas, don ta samu rinjaye a wannan zabe da aka gudanar.

Da yawa dai daga cikin masu nazarin siyasa ta kasa da kasa dake yankin gabas ta tsakiya, na kallon wannan mataki da kasar ta Amurka ta dauka a matsayin aikin baban giwa, wanda a ganin su a maimakon hakan da Amurka matsawa Israela tayi don ta ci gaba da sako fursunonin yankin da take tsare dasu, a hannu daya kuma da tashin yan kaka gida a yankunan na Palasdinawa, wanda hakan a ganin su daya taimakawa jamiyyar ta Fatah ta samu galaba a wannan zabe.

Ire iren wadan nan matakai da kasar ta Amurka ta dauka a cewar masu kalailaice harkokin siyasa a yankin, nada nasaba ne da irin yadda ake kallon kungiyyar ta Hamas ne.

A misali kasar Amurka da Israela da kawayen su na kallon kungiyyar ne a matsayin ta yan ta´adda, a inda a hannu daya wasu ke kallon ta a matsayin kungiyyar gwagwarmayar kwatowa Palasdinawa yan cin su daga kasar Israela.

Bugu da kari masu nazarin siyasar sun kuma shaidar da cewa, wannan nasara da kungiyyar ta Hamas ta samu,ya karawa kunngiyoyi na masu tsattsauran ra´ayi kwarin gwiwa,a misali irin su Jam´iyyar Brotherhood dake Masar data Yan sunni da shi´a dake iraqi a hannu daya kuma data Hizboullah dake Lebanon.

A lokacin da yake jawabi bayan fitowar sakamakon zaben,shugaba Bush na Amurka ya tabbatar da cewa babu yadda za´ayi a hada batun zaman lafiya da tashin hankali guri guda.A don haka Mr Bush yace matukar kungiyyar ta Hamas na son taka rawar cimma sulhu, to dole ne ta kwance damarar yaki akan Israela.

Shi ma dai Mr Geoffrey Kemp, wani masani akan harkokin siyasar gabas ta tsakiya, cewa yayi akwai bukatar kungiyyar ta Hamas tayi dogon tunani na ko dai ta ajiye makamai don kwance damarar yaki ko kuma akasin hakan, domin yin hakan a cewar sa zai taimaka wajen fahimtar inda sabuwar gwamnatin da za a kafa ta dosa.

Duk da cewa babu wani lokaci da kungiyyar ta Hamas ta fito fili ta bayyana cewa zata kwance damara, daya daga cikin shugabannin ta wato Mahmod Zahar cewa yayi kungiyyar a shirye take ta cimma yarjeniyoyin sulhu da kasar ta Israela.