1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NDA: Mu maka kai hari a yakin Niger Delta

Mouhamadou Awal BalarabeMay 26, 2016

Wata sabuwar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta ta Niger Delta Avengers ta ce ita ta fasa bututun man Chevron. Sai dai gwamnatin Buhari na daukansu a matsayin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1IuYC
Nigeria Piraterie
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu tsagerun yankin Niger Delta na tarayyar Najeriya sun yi amfani da kafar sadarwa ta zamani ta Twitter wajen daukar alhakin fasa bututun mai na kamfanin Chevron. ‘Ya’yan wannan kungiya da ke kiran kanta "Niger Delta Avengers" ko NDA a takaice sun ninka hare-hare a makonnin da suka gabata don matsa wa gwamnati lamba domin ta biya musu wasu bukatunsu, lamarin da ya kawo cikas ga harkar hako man fetur a yankin.

.Ya zuwa yanzu dai kamfanin mai na Chevron bai ce uffan kan wannan sako ba, amma kuma gwamnatin Najeriya na daukar tsagerun yankin Niger Delta a matsayin 'yan ta'adda.Tuni ma ta tura da jami’an tsaro domin su karya lagwansu.

Shugabannin kungiyar NDA sun yi korafin cewar yankin Niger Delta ba ya cin gajiyar arzikin fetur da Najeriya ta dogara da shi wajen shigar da kashi 70 cikin 100 na kudin da ta ke samu. Sai dai tsaffin tsageru na MEND sun yi kira ga takwarorinsu na NDA da su dakatar da hare-haren da suke kaiwa.