1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman afuwa game da ta'asar kisa a Ireland

June 16, 2010

Cameron, ya nemi afuwa game da kisan da ya auku a Ireland a 1972.

https://p.dw.com/p/NrzY
Brian Cowen, fraministan Ireland.Hoto: AP

Fraministan Ireland, Brian Cowen ya amince da neman afuwar da fraministan Birtaniya, David Cameron yayi game da kisan da dakarun Birtaniya suka yi ga wasu 'yan zanga-zangar Katolika guda 14 a garin Londonberry da ke arewacin ƙasar ta Ireland a shekarar 1972. Cowen yace neman afuwar wani abu ne daka iya kau da raɗaɗin rashin adalci da ake dade ana fama da shi. Jawabin na Cameron dai ya zo ne sakamakon buga rahoton da aka dade ana dakonsa bayan da aka shafe shekaru 12 ana gudanar da bincika akan wannan ta'asar da aka yi fi sani da suna "Bloody Sunday". Cameron ya faɗa wa majalisar dokokin Birtaniya cewa ko shakka babu sakamkon binciken da aka yi wa suna "Saville Report" ya bayyanar da wannan kisa tamkar ɗanyen hukunci. Ya ce babu wanda ya riƙa makami daga cikin waɗanda aka kashen, kuma babu wani kashedi da aka yi wa sojoji. A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 1972 ne sojojin Birtaniya suka buɗe wuta akan 'yan zanga-zangar sannan daga bisani suka ce 'yan zanga-zangar sun riƙe makamai.

Mwallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu