1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen Boko Haram a Tafkin Chadi

Ubale Musa / LMJMay 13, 2016

Dinbin fatan da Tarayyar Najeriya da makwabtanta ke da shi, gabanin fara wani babban taro na tsaro da nufin kawo karshen annobar Boko Haram da tai kamari a cikin yankin Tafkin Chadi.

https://p.dw.com/p/1Ineg
Taron yankin Tafkin Chadi a Abuja a bara
Taron yankin Tafkin Chadi a Abuja a baraHoto: State House, Abuja

Fatan da wadannan kasashe ke fda shi dai ya danganci samun agajin kudi da kaya na bukatu, da nufin sake farfado da rayuwa bayan rikicin da ya hallaka mutane sama da 20,000 ya kuma raba miliyoyi da muhallinsu. Taron na Abuja da ke zaman na biyu tun bayan dan uwansa na birnin Paris, na zaman damar tsallen murna da Owambe ga kasashen yankin Tafkin Chadin da ke tunanin cin karfi na kungiyar ta Boko Haram. Shekaru biyu bayan taron Paris din, kasashen hudu da ke tsakiyar rikicin dai sun nasarar rage aiyyuka na kungiyar daga kamawa da iko da yankuna ya zuwa yakin sari ka noke a wurare na kalilan.

Nasarar birnin Paris din dai ce ake ta'allaka wa da bude sabon babin da ya kai ga hadin kai na sahihi, dama tunkarar matsalar da zuciya guda a tsakanin Najeriyar da makwabtan nata da a baya take zargi da jan kafa wajen tunkarar matsalar.

Sojoji na ci gaba da yakar Boko Haram
Sojoji na ci gaba da yakar Boko HaramHoto: PATRICK FORT/AFP/Getty Images

Muhimmancin taron ga Najeriya

To sai dai kuma ko bayan kokari na karfi na hatsi ta siyasa ma dai, taron na da muhimmancin gaske ga Tarayyar Najeriyar a fadar ministan tsaron kasar janar Mansur Dan Ali mai ritaya da ya ce kasar ta Najeriya na neman hanyoyin kara hadin kai tsakaninta da makwabtan kasashen yankin na Tafkin Chadi da dukkaninsu ke zaman reno na Faransa. Makomar mutane sama da miliyan biyu da 800,000 da yakin ya raba da muhallinsu, dama kokari na sake ginin yankunan da ke lalace, gami da musaya ta fursononin yaki ne dai ake sa ran za su dauki hankalin mahalarta taron da ko bayan kasashen hudu suka kunshi Faransa da Ingila da kuma Amirka. Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Tarayyar Najeriyar da Majalisar Dinkin duniya dama Tarayyar Turai, ya nunar da cewa ana bukatar akalla dalar Amirka Miliyan 9,000 kafin sake tada komada a jihohi uku na Tarayyar Najeriya in da yakin yafi tasiri.

Kokarin sake farfado da Tafkin Chadi

Kuma daga dukkan alamu taron zai kalli yi wuwar sake farfado da Tafkin Chadi da ake ta'llaka kafewar sa da bulla dama kamarin annobar ta Boko Hharam. Kasa da kashi 10 cikin 100 na tafkin da ke zaman hanya ta rayuwar mutane kusan miliyan 30 ne dai ya rage yanzu. Abun kuma da ya kai ga kara ta'azzara fatara da ma talauci a cikin yanki da kuma haihuwar akidar ta ta'addanci. Kakakin gwamnatin kasar ta Najeriya Malam Garba Shehu dai ya bayyana cewa kasashen yankin ba su da kudaden da ake bukata da nufin sake farfado da rayuwar al'ummar Tafkin na Chadi a yanzu. To sai dai kuma jerin matsaloli na kudi dama dogaro da hajar man fetur, na neman mayar da duk wani kokari na samun sauyi a cikin yankin yin kama da mafarkin tsakiyar rana.

Irin ta'adin da Boko Haram ke yi a Najeriya da makwabtanta
Irin ta'adin da Boko Haram ke yi a Najeriya da makwabtantaHoto: Reuters/M. Nako