1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman daidaituwa kan batun yan gudun hijira a Turai

Umaru AliyuJuly 15, 2010

Ministocin cikin gida na kungiyar hadin kan Turai sun yi taro a Brüssels, game da neman cimma manufa daya kan yan gudun hijira

https://p.dw.com/p/OMc3
Yan gudun hijira daga kasashe masu tasowaHoto: PA/dpa

Bayan lokaci mai tsawo da aka dauka ba tare da kasashen na kungiyar hadin kan Tuai sun tabo batun na yan gudun hjijira ba, kasar Belgium, dake shugabancin kungiyar a yanzu, ta gabatar da wani sabon yumkuri na ganin kasashe ashirin da bakwai sun daidaita a game da makomar yan gudun hijira dake shigowa cikin su suna neman mafakar siyasa. Burin kasar ta Belgium shine a cimma wata manufa ta bai-daya tsakanin dukkanin kasashen, a game da kula da yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa, nan da shekara ta 2012.

Tun a shekara ta 2008 da shekara ta 2009, hukumar kungiyar hadin kan Turai ta gabatar da shawarwari a game da yadda za'a daidaita batun na yan gudun hijira a kungiyar, amma wasu kasashe, musmaman Jamus da Faransa suka hana amincewa da wadannan shawarwari, sakamakon adawar su. Gwamnatin Jamus tana baiyana tsoron cewar shimfida sharudda masu sassauci a game da masu neman mafakar siyasa, yana iya haddasa cikas ga nata dokokin masu tsanani kan yan gudun hijira.

Daga cikin shawarwarin da hukumar kungiyar hadin kan Turai ta gabatar, har akwai kawar da matakin hamzarta maida yan gudun hijira kasashen su na asali, ko kuma nuna banbanci ga masu neman mafakar siyasar a rayuwar yau da kullum a kasashen da suka shiga. Kazalika, hukumar tana neman a karfafa matsayin yan gudun hijiran ta fuskar shari'a, tare da kyale kananan yara da basu kai shekaru goma sha takwas ba su zauna tareda iyayen su dake neman mafakar siyasa. Ole Schröder, karamin minista a ma'aikatar cikin gidan Jamus yace kasar sa tana iya goyon bayan shirin kafa wani ofishi da zai rika baiwa kasashen na Turai shawara kan batun yan gudun hijira to amma yace:

A game da sauran shawarwarin da hukumar kungiyar hadin kan Turai ta gabatar har yanzu muna cikin shawarwari ne masu sarkakiya. Mu Jamusawa akwai fannoni da dama a wadamnnan shawarwari da muke shakkar dacewar su, musamman kan kudirorin da ake tattaunawa kansu yanzu.

Makim Sochi, dan kasar Togo da ya shigo nan Jamus yana neman mafakar siyasa, yace a wannan kai da komo, bai san matsayin sa ba na neman mafakar siyasa.

Yace shin me zai faru gareni, ko ma zan sami damar cimma burin samun amincewa a matsayin dan gudun hijira, ko kuwa washegari yan sanda zasu zo ne su tafi dani, su tura ni gida. Duka wadannan tambayoyi ne dake daga mani hankali, kuma abubuwa ne dake lalata mutum.

Dangane da haka, karamin minista a ma'aikatar cikin gida na Jamus, Ole Schröder yake cewa:

Saboda muna son ci gaba da manufofin mu kan batun yan gudun hijira, wadanda muka ga amfani da cewar su, hakan ba yana nufin duk wadanda suke bukatar kariya daga wurin mu, wadanda ake gallaza masu ta fuskar siyasa ba zasu sami kariyar da suke bukata bane, amma kuma duk wadanda suke kokarin amfani da manfofin mu na yan gudun hijira domin cin ribar kansu, ba kuwa zasu sami kariya daga garemu ba.

A nashi bangaren karamin minista a ma'aikatar cikin gidan Belgium, Melchior Wathelet yace daidaita batun na yan gudun hijira tsakanin kasashen kungiyar hadin kan Turai yana daga cikin abubuwan da za'a fi basu fifiko a kungiyar hadin kan Turai da ita kanta Belgium, a tsawon shugabancin ta ga wannan kungiya.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Ahmed Tijani Lawal