1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman hanyoyin magance matsalolin almajiranci

April 13, 2017

Wata hadakar Kungiyoyin kare ‘yancin yara a Nigeria da na fararen hula sun bukaci gwamnatin tarayyar kan daukar matakan magance karuwar kwararowar kananan yara almajirai.

https://p.dw.com/p/2bDEI
Angola Slum Kinanga in Luanda
Hoto: DW/N. Sul d'Angola

Kananan yara almajirai ‘yan kasa da shekaru 5 ke gararamba kan tituna da tashoshin mota domin barace-barace, lamarin da ya sanya kungiyoyi ke fafatukar tabbatar da ganin cewa an magance kwararowar kananan yara almajirai daga karkara zuwa birane wadanda ke fadawa tarkwan matsafa da masu fyade da sauran wahalhalun da suke shiga domin neman na abinci, wanda a saboda haka ne hadakar kungiyoyin kare ‘yanci da rayuwa a Nigeria ta bukaci gwamnatin tarayyar da ta dauki mataki cikin gaggawa.

Mr Diji Haruna Obadiya shi ne shugaban Network of Child Protection da ke nuni da cewa ya kamata gwamnati ta magance yadda ake safarar kananan yara almajirai daga wannan jahar zuwa wancen jahar ba tare da hukunta masu yin jigilar wadannan yara ba zuwa gaban koliya. Shi kowa Dr Auwal Abdullahi Aliyu da ke zama shugaban kungiyoyin fafaren hula a Kaduna ya ce lallai dai kam lokaci ya yi da gwamnatin za ta kawo karshen wahalhalun da ake jefa kananan yara almajirai.

Alltagsleben im Flüchtlings-Camp Malkohi, Nigeria
Hoto: DW/J.-P. Scholz

Gami da wannan matsalar dai tuni suma dai manyan Malaman addinin Islama a Nigeria irin su Mallam Mohammad Tukur Abdulsalam Unguwar Rimi ke janyo hankalin iyaye ga amanar da Allah ya ba su.

Yanzu haka dai a sakamakon wadannan matsaloli ne ya sanya gwamnatin Jihar Kaduna shiga farautar wadannan kananan yara mabarata almajirai domin mayar da su hannun iyayensu kamar dai yadda Hajiya Hafsat Mohammed Baba kwaminiyar mata da kananan yara ta jihar ke kara bayar da haske. Fatar kungiyoyin kare ‘yancin yaraan ita ce, ganin an fargar da iyayen kananan yara mazauna karkara bisa ga makomar da suke jafa yaransu.