1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman ikon hawa kujerar naki a kwamitin Sulhu da Jamus ke yi

Mohammad Nasiru AwalDecember 10, 2004

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya jaddada bukatar kasar game da samun ´yancin hawa kujerar naki a kwamitin sulhu na MDD.

https://p.dw.com/p/BveF
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da Firaministan Japan Yunichiro Koizumi a taron manema labarai a birnin Tokyo
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da Firaministan Japan Yunichiro Koizumi a taron manema labarai a birnin TokyoHoto: AP

Kamata yayi gwamnatin fadar White House a birnin Washington ta zuba ruwa kasa ta sha saboda doki da kuma murna. Domin da farko dan sakatare janar na MDD Kofi Annan wato Kojo Annan ya barowa ubansa wani abin kunya dangane da wata tabargaza da ya tabka, sai kuma wadannnan kalaman daga nahiyar Asiya, wanda ko shakka babu ka iya janyo rugujewar shirin yiwa MDD garambawul, shirin da ba ya samun goyon baya daga Amirka, musamman ganin cewar hakan ka iya rage mata wani iko.

Canje-canjen da ake shirin yiwa MDD din ya hada da fadada kwamitin sulhu don ya dace da halin da ake ciki a wannan karni na 21. Gwamnatin birnin Berlin kuwa ta sanya burin samun shiga cikin kwamitin sulhun, wanda Jamus ta cancanci samu musamman bisa la´akari da yawan gudummawar kudi da take ba MDD da kuma aikin sake gina kasar Afghanistan da dakarun ta ke yi.

A dangane da haka Jamus karkashin jagorancin jakadanta a MDD Gunther Pleuger da ministan harkokin waje Joschka Fischer sun yi ta kai gwauro suna kai mari da zummar samarwa Jamus din goyon bayan kashi 2 cikin 3 na yawan kasashen majalisar don cimma wannan buri da ta sa a gaba.

To amma tun ba´a kai ko-ina ba majalisar dokoki da ta dattijan Amirka, inda jam´iyar Republicans ta shugaba Bush ke da rinjaye ba su yi wata-wata ba wajen kin sanya hannu akan kudurin da ake bukata bisa manufar yiwa MDD garambawul. Bugu da kari an fuskanci mummunar adawa dangane da bukatar da kasashen Japan, Indiya, Brazil da Jamus suka nuna na neman cikakken wakilci a kwamitin sulhu. Duk da takatsatsan da suka rika yi har yanzu wadannan kasashe 4 ba su cimma wani abin a zo a gani bisa manufa ba.

Amma a jawabin da yayi a gun taron tattalin arziki a birnin Tokyo, SGJ Gerhard Schröder bai nuna wani sassauci ba, domin ya fito fili ya jaddada bukatar Jamus na samun ikon hawa kujerar naki cikin kwamitin sulhu. To sai dai shugaban gwamnatin ba yi wadannan kalaman a lokacin da ya dace ba. Ko kuma shugaban gwamnatin na Jamus bai san cewar da yawa daga cikin kasashe 191 na MDD na adawa da ikon hawa kujerar naki ba ne? Ko kuma ya manta da cewa hatta shi kanshi sakatare janar na MDD Kofi Annan ya na bin hanyoyi ne na diplomasiyya wajen ganin an rage karfin ikon kasashe 5 din dake da hawa hujerar naki ba ne? Da kamata yayi, mista Schröder ya kama bakinshi yayi shiru, domin ko shakka babu kasashen dake adawa da yiwa kwamitin sulhun kwaskwarima sun harzuka da wadannan kalaman, kuma bisa ga dukkan alamu zasu dauki matakai don hana a samu rinjayen kashi 2 cikin 3 na yawan kuri´un da ake bukata a babbar mashawartar MDD kafin a aiwatar da wani canji mai ma´ana cikin kwamitin sulhu.