1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman kawo cikas ga taimakawa kasashe masu tasowa a taron kungiyar ciniki ta duniya

Hauwa Abubakar AjejeDecember 14, 2005

Komishinan ciniki na kungiyar taraiyar turai yayi gargadin cewa akwai alamun cewa ,taron kungiyar ciniki ta duniya dake gudana yanzu ba zai samu nasarar taimakawa kasashe masu tasowa ba,kamar yadda akayi tsammani a baya.

https://p.dw.com/p/Bu3P
Hoto: AP

Kodayake komishinan ciniki na kungiyar ta ciniki Peter Mandelson bai sunayen kasashe da suke kawo cikas ga wannan batu ba,amma jamian diplomasiya na turai sunce kasashen Amurka da Japan suna nokewa game da batun kawadda haraji daga kan kayayiyakinsu da kasashe masu tasowa suke bukata.

Mandelson ya fadawa taron manema labarai cewa,ya damu da cewa akwai yar matsala a batun shirin taimakawa kasashe masu tasowa,wanda yace muddin dai basu cimma wannan nasara ba to kuwa babu anfanin wannan taron da sukeyi a Hong Kong.

Kusan membobi 150 na kungiya a halin yanzu sun rigaya sun cire fatar cewa zaa samarda yarjejeniya ta kawadda shingayen kasuwanci da haraji akan kasashe masu tasowa,wanda ada shine batu da taron yake son cimma matsaya a kansa.

Manyan masu masanaantun auduga na Afrika tuni sunyi gargadin cewa gwamnatocinsu bazasu yadda da wata yarjejeniya dab a zata hada da rage haraji akan hajojinsu ba,musamman na kasar Amurka,wanda suka ce suke hana su takara da takwarorinsu a kasuwannanin duniya.

Kin amincewa Kungiyar Karaiyar Turai akan batun rangwame na harajin anfanin gona,shine ya zamo abinda ya hana ruwa gudu a taron baya da akayi a Doha,haka zalika wasu suna ganin cewa taron Brussels daya shawarta sassutawa kasashe masu tasowa,wani yunkuri na kawadda hankulan jamaa daga kan taron na Hong Kong.

Babban dai abinda taron ya shawarta a Brussels,shine kawadda haraji da kuma bude hanoyin kasuwanci akan kasashen kungiyar 49 mafiya talauci.

Sai dai jamian ciniki a taron sunce, kasar Amurka tana neman kauracewa batun budewa kasashe matalauta kofofin kasuwanci musamman a fannonin,tufafi,sukari da auduga,haka kuma kasar Japan bata son bude kasuwarta ta shinkafa ga kasashen masu tasowa.

Haka kuma Washington da Tokyo,sun nuna damuwarsu game da maiyarda yarjejeniyar ta zamo ta dindindin,wadda suka ce hakan zai iya hana su aiwatar da wasu gyare gyare bisa canje canje a tattalin arzikinsu na cikin gida.

A yau din nan kasar Amurka tace,zata ribanya taimako da take baiwa kasashe masu tasowa zuwa dala biliyan 2 da digo 7 a kowace shekara zuwa 2010,ita kuma Japan a nata bangare ta rigaya ta alkawarta taimakawa da dala biliyan 10 ga kasashe masu tasowa su bunkasa harkokin kasuwancinsu.

Sai dai kuma kungiyar bada taimako ta Oxfam ta Burtaniya, ta baiyana shakkunta game da wadannan alkawura,tana mai cewa yawancin kudaden na taimako ne da aka rigaya aka alkawarta tun a baya,saboda haka abinda zasuiy shine kawai sauya masu akala daga shirye da aka tsara tun farko,wadda kuma a cewar kungiyar yin hakan zai tilastawa kasashe matalauta yin zabi tsakanin taimakoa fanning kasuwanci ko kuma muhimman abubuwa kamar magunguna da ilmi.

Oxfam tace ana bukatar taimako a fannin kasuwanci amma bai kamata ya zamo taimako da zai maye gurbin taimako kan wasu muhimman abubuwa ba.