1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman magance rikicin siyasar Abiri Kwas

March 18, 2010

Hukumomin Abiri Kwas sun ɗibar ma kansu wa´adin watanni biyu domin gudanar da zaɓen gama gari.

https://p.dw.com/p/MVh5
Shugaba Gbagbo na Abiri KwasHoto: AP

Hukumomin Abiri Kwas ko kuma Kot Divuwar sun tsayar da watan Afrilu, ko kuma na Mayu ya kasance lokacin gudanar da zaɓen gama gari a ƙasar. Jakadan na Abiri Kwas a Majalisar Ɗinkin Duniya wato Alcide Djedje ya shaida wa kwamitin sulhu cewa jam´iyun siyasa ba su kai ga cimma matsaya game da tartibiyar rana da zaɓen zai gudana ba. Amma kuma ɓangarorin daban daban sun nunar da cewa bai kamata a zarta watanni biyu masu zuwa ba tare da mayar da ƙasar kan turbar demokaraɗiya ba.

Tun shekaru biyar da suka gabata ne wa´adin mulki shugaba Gbagbo ya shuɗe. Ammma kuma rikicin siyasa ya sa aka yi ta ɗage zaɓen. Hukumomin na Kot divuwar sun sake ɗage lokacin gudanar da zaɓen ne, bayan almundahanar da aka gano an tafka wajen yin rajistar sunayen bogi ga fiye da mutane dubu 400 domin su ka'ɗa ƙuri'a.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala