1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman sulhu tsakanin Jamus da Turkiyya

March 8, 2017

Ministan harkokin waje na Jamus Sigmar Gabriel na kokarin kashe wutar rikicin da ta taso tsakanin Jamus da Turkiyya a kan maganar kada kuri'ar raba gardama don karawa shugaba Recep Tayyip Erdogan karfin iko.

https://p.dw.com/p/2Ype7
Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel a hagu tare da takwaran aikinsa na Turkiyya Mevlüt Cavusoglu a dama
Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel a hagu tare da takwaran aikinsa na Turkiyya Mevlüt Cavusoglu a damaHoto: picture-alliance/AA/C. Ozdel

A lokacin wata ganawa da ministan ya yi da takwararnsa na Turkiyya Mevlüt Cavusoglu a birnin Berlin,ministan ya ce akwai wata dama ta sake dawo da hulda tsakanin kasashen biyu kamar yada take a da:'' Muna so mu samu zutuwa da wannan kasa ta Turkiyya domin shawo kan barakar da ke tsakaninmu da su, cikin ruwan sanhi saboda mu aminansu ne.Sama da mako guda ke'nan da ake kai ruwa rana tsakanin hukumomin na Jamus da na Turkiyya,bayan da gwamnatin Jamus ta haramta wani gangami na magoya bayan Erdogan masu goyon bayan kuri'ar rabar gardama a kan kudin tsarin mulkin na Turkiyya.A kasar ta Jamus dai akwai 'yan Turkiyya da ke zaune masu kada kuri'a sama da miliyan daya.