1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman zaman lafiya a Darfur

July 31, 2010

MƊD ta yi kira ga 'yan tawayen Darfur da su shiga tattaunawar zaman lafiya

https://p.dw.com/p/OYnI
'Yan gudun hijirar DarfurHoto: AP

Kwamitin Sulhun majalisar Ɗinkin Duniya yayi kira da a daina tashe tashen hankula nan-take a Darfur mai fama da rigingimu. Kwamitin Sulhun ya kuma buƙaci dukkan ƙungiyoyin 'yan tawaye da su shiga cikin tattaunawar neman zaman lafiya da nufin kawo ƙarshen rikicin da aka shafe shekaru bakwai ana yi a wannan yanki dake yammacin ƙasar Sudan. A cikin wani ƙuduri da ya samu amincewar dukkan wakilai, Kwamitin Sulhun yayi amfani da kalamai masu tsauri yana mai yin tir da ƙungiyoyin 'yan tawayen da suka ƙi shiga cikin shirin na neman wanzuwar zaman lafiya. Ƙudurin ya tsawaita wa'adin rundunar haɗin guiwa tsakanin Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka a Darfur har izuwa ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 2011, sannan yayi kira ga dakarun da su ba da fifiko wajen kare fararen hula da tabbatarwa ma'aikatan agaji sun kai taimako cikin kwanciyar hankali.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar