1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya ziyarci Amurika

March 23, 2010

Benjamin Netanyahu yayi jawabi a taron shekara shekara na Ƙungiyar yahudawan Amurika

https://p.dw.com/p/MZhU
Jawabin Netanyahu a gaban Ƙungiyar yahudawan AmurikaHoto: AP

Firaministan Isra´ila Benjamen Netanyahu ya gabatar da jawabi ga taron shekara shekara na wata ƙungiyar ƙasar Amurka dake goyon bayan Isra´ila. A lokacin jawabin nasa a jiya, Netanyahu ya ƙara jaddada dangantakar dake tsakanin yahudawa da birnin Qudus tare kuma da kare matakan da Isra´ilan ke ɗauka a yankunan Palasɗinawa. Wannan jawabi na Firaministan yazo ne a daidai lokacin da danganta tsakanin Isra´ilan da Amurka ta shiga wani hali na tsaka mai wuya sakamakon ƙememen da Isra´ila tayi da kiraye kirayen da ake mata ta dakatar da shirin gina matsugunan yahudawa ´yan kama guri zauna 1,600 a yankunan da take taƙaddama tsakanin ta da Palasɗinawa. Matakin da kuma tunda fari Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace yana barazana ga shirin zaman lafiyan yankin Gabas ta Tsakiya. koda yake a jawabin data gabatar wajen taron ƙungiyar ta yahudawa dake birnin Washington DC, tunda farko Sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ila duk kuwa da irin matakan da Isra'ilan ke ɗauka na yin ƙafan angulu ga aiyukan samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. A wani lokaci a yau ne dai Netanyahu zai gana da shugaba Barack Obama na Amurka a wani yunƙuri na daidaita matsalar cacar baka da akeyi tsakanin ƙasashen biyu.

Mawwallafi: Babangida Jibril Edita: Yahouza Sadissou Madobi