1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Niger: Alkalai na son a hukunta Bazoum

Abdoulaye Mammane Amadou/ASNovember 30, 2015

Kungiyar alkalai a Nijar na son a kwabewa minista a fadar shugaban kasa Bazoum Mohammed rigar kariya don gurfana gaban kotu bisa kokarin raba hadin kan 'yan kasa.

https://p.dw.com/p/1HEry
Außenminister der Republik Niger Mohamed Bazoum
Hoto: DW/T.Mösch

Kungiyar alkalan da ake kira SAMAN dai ta ce daukar kokarin da ta ke yi na ganin Bazoum Mohammed ya gurfana gaban kotu na da nasaba da wasu kalamai da ya yi wanda ka iya tada zaune tsaye da kana za su iya jawo rabuwar kawuna tsakanin al'ummar kasar. Wannan kalamai dai inji kungiyar su ne irinsu mafi muni da wani babban jami’in gwamnati ya yi.

Baya ga wadannan maganganu da kungiyar ta ce Bazoum din ya yi marasa dadi, a hannu guda ta ce maganar da ya yi kan cewar wasu alkalai sun karbi toshiya wajen zartar da shari’ar da ake yi kan badakalar nan ta safarar jarirrai da ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin kasar da aikatawa abu ne dai bai dace kuma kungiyar ba za ta lamunta ba kamar yadda mukaddashin magatakardar kungiyar ta SAMAN mai shari'a Aboubakar Nouhou ya shaidawa DW.

Mai shari'a Nouhou ya ce ''a matsayin shi na minista (Bazoum Mohammed) idan har bai yi kalaman da za su hada kan kasa ba to bai kamata ya yi wasu kalamai da za su raba kan al'umma ba saboda haka mun yi kira ga babban mai gabatar da kara ya sa a tuhume shi don ya a hukunta''

Shi dai Bazoum Mohammed wanda yanzu haka shi ne ke shugabantar jam'iyya mai mulki a Nijar din ya bayyana a wata jarida mai suna Jeune Afrique cewar tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Hama Amadou kan yi yunkurin tayar da fitina a duk lokacin da ya ke bangaren adawa kana ya na yin kalaman da ke raba kawunan 'yan siyasa.

Hama Amadou nigrischer Oppositionspolitiker
Daga cikin kalaman da Bazoum ya yi har da zargin Hama Amadou da kokarin raba kan 'yan siyasa.Hoto: DW/S. Boukari
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Alkalai na son ganin shugaba Muhammadou Issoufu ya bada hadin kai wajen hukunta Bazoum.Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images