1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Niger Delta: An nemi dakatar da kai hari

Ahmed SalisuMay 21, 2016

Tsofaffin 'yan bindigar yankin Niger Delta a Najeriya sun bukaci 'yan yankin da suke kai hare-hare wajen tonon mai da iskar gas da su gaggauta dakatar da yin hakan.

https://p.dw.com/p/1IsJa
Nigerdelta Angriff Rebellen
Hoto: picture alliance/dpa

'Yan bindigar na tsohuwar kungiyar nan ta MEND suka ce wannan hare-haren ba su da wani alfanu kuma yin hakan yunkuri ne na kawar da hankalin gwamnatin kasar daga yin aikin da ya kamata ta yi wa al'umma.

A wata sanarwa da tsofaffin 'yan tawayen suka fidda, sun ce ya kamata a dafa wa Shugaba Muhammadu Buhari don samun sukunin cika alkawuran da ya dauka kan yankin na Niger Delta. A ranar Juma'a dai gwamnatin ta Najeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da tsaurara matakan tsaro kan wuraren da ake tonon mai a yankin bayan da 'yan bidiga suka dawo da kai hare-hare.