1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria da Senegal na sake tunani kan Darfur

October 2, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9h

Mdd tayi fatan cewa harin da aka kaiwa rundunar sojin Au a Darfur, ba zai kawo gibi wajen aikin da suka sa a gaba ba a yankin.Karamin sakataren aikin kiyaye zaman lafiya na Mdd, Mr Jean- Marie Guehenno,yace tunanin wani abu na daban sababin abin da aka sa a gaba, abu ne daka iya dawo da hannun agogo baya. Kasashen Nigeria da Senegal dai dake da yawan soji a cikin rundunar ta Au, sunce a yanzu haka suna nazarin irin rawar da zasu taka a yankin na Darfur a nan gaba. Hakan kuwa ya biyo bayan harin da aka kaiwa rundunar ne, wanda sakamakon haka suka rasa wasu daga cikin sojin su, bayan da wasu da dama suka jikkata.Kai wannan hari a cewar Jami´in na Mdd, abune daya karawa Mdd kaimi na samar da ingantattun kayan aiki ga dakarun hadin gwiwa da za´a aike izuwa yankin na Darfur nan daba dadewa ba.