1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria na ci gaba da yaki da cutar murar tasuntsaye

February 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7J

Gwamnatin tarayyar Nigeria na ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye a fadin kasar baki daya.

Hakan kuwa yazo ne bayan da cutar ta kara bulla a jihohin Katsina da Zamfara,wanda hakan ya kawo jumlatan jihohi 7 da suka fuskanci bullar cutar mai nau´in H5N1 a kasar.

Hukumomin lafiya na kasar da suka tabbatar da wannan labari sun kuma shaidar da cewa a tun bayan bullar cutar har yanzu babu mur´tum guda daya kamu da cutar.

Bugu da kari sanarwar ta kuma yi nuni da cewa har yanzu ana ci gaba da kashe miliyoyin kaji na gonaki daban daban da ake zaton sun kamu da wannan cuta, a matsayin rigakafi wanda hausawa kann ce yafi magani.