1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria ta ƙudiri aniyar samar da makamashin nukiliya

August 1, 2006
https://p.dw.com/p/BuoF

Nigeria ta ɗauki wani mataki a kokarin ta na mallakar makamashin nukiliya domin amfanin alúma yayin da ta rantsar da yan hukumar zartarwa na hukumar makamashi ta ƙasa. Shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo wanda ya ƙaddamar da yan hukumar yace zaá yi amfani da makamashi ne wajen samar da wutar lantarki da inganta harkar noma da sarrafa magunguna da kuma wasu shaánin binciken kimiyya. Nigeriar tun a watan Satumba na shekarar 2004 ta kafa cibiyar binciken kimiyyar makamashin nukiliya wanda shugaban hukumar makamashin nukiliyar ta MDD Mohammed El-Baradei ya ziyarta. Shugaban Nigeriar Olusegun Obasanjo yace Nigeria bata nufin ƙera makamin ƙare dangi. Yana mai cewa wajibi ne ƙasar ta yi tanadin makamashi don gaba domin rage dogaro a kan albarkatun man petur wanda yana iya gushewa. Nigeriar dai na daga cikin ƙasashen Afrika masu arzikin mai a duniya.