1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria ta fara kwashe dakarun ta daga yankin Bakassi

August 8, 2006
https://p.dw.com/p/BunT

Gwamnatin Nigeria ta fara janye dakarun sojin ta data jibge a yankin Bakassi, mai arzikin man fetur, wanda take rikici a kann sa da kasar Kamaru.

Kamfannin dillancin labaru na AFP ya rawaito birgediya janar Felix Chukuma na fadin cewa, an fara kwashe sojin ne don cika alkawarin da aka daukarwa Mdd na barin yankin kwata kwata ,a cikin kwanaki 60.

An dai cimma wannan yarjejeniyar ne a tsakanin shugaba Obasanjo da Paul Biya na Kamaru a ranar 12 ga watan yuni, a can birnin New york na Amurka , bisa sa idon sakataren Mdd, Mr Kofi Anan.

Karkashin yarjejeniyar, Nigeria zata kwashe sojojin nata ne daga yankin, cikin kwanaki 60, idan kuma hali yayi zata iya kara kwanaki 30.

A dai shekara ta 2002 ne kotun kasa da kasa dake birnin Hugue ta yanke hukuncin mika yankin na Bakassi izuwa kasar ta Kamaru.