1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An amince a kwaskware kundin tsarin mulki

Abdoulaye Mamane Amadou
May 30, 2017

Majalisar dokokin kasar ta amince da kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin wanda a can baya ya haifar da cece kuce, an dai amince da gyaran fuskar ba tare da halartar 'yan adawa ba suna cewa tsarin ya sabawa ka’ida

https://p.dw.com/p/2drLe
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Galibin ayoyin  shida da majalisar dokoki ta yi wa gyaran fuska a cikin kudin tsarin mulkin sun shafi batutuwan zabe da wa’adinsa, da ma batutuwan kai koke-koke a gaban kotun tsarin mulki, da zaben maye gurbi na majalisar dokoki idan har shugaban kasa ya dauki kudurin rusa ta, da na maye gurbin shugaban kasa idan Allah ya yi masa cikawa. Bisa gagarumin rinjaye ne dai majalisar ta dokokin Nijer ta aminta da kawo sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar a wani yunkuri na kawo masalaha dangance da rigingimun da a ka lura da su a baya, masu nasaba da zabubbukan game gari musamman ma na shugaban kasa zagaye na biyu. Duba da karamcin wa’adin kwanaki a gabanin karshen wa’adin shugaban kasa, don shirya zaben majalisar ta aminta da tsawaita kwanakin daga 90 zuwa 120 ga sabuwar ayar dokar ta kundin tsarin mulki

Malam Bazoum Mohamed ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar ne: "Yace wannan ne muka ga ya fi dacewa a dauki kwanaki 120 kafin karshen wa’adin shugaban kasa a shirya zaben, kuma na bayyana maku hujjojin da suka sa aka shirya tsare tsaren ba wai wata Magana bace ta siyasa"

Kamar yadda suka yi alkawali a baya dai yan adawa a majalisun dokokin gungun adawa sun kauracewa shiga taron kana suna mai cewar sauye sauyen kundin tsarin mulkin ba komai ba ne face wata manufa da gwamntin kasar ke son cimma ta hanyar amfani da matsayinta da ke a majalisar dokoki.

 Wannan dai shi ne karon farko kenan da gwamnatin ta bukaci kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma yanzu hakan ya ke ci gaba da haifar da ja in ja tsakanin bangaren adawar da na masu rinjaye. Yanzu haka dai hankalin 'yan kasar ya karkata dangance da yadda za ta kaya a gaba, duba da korafe-korafen kauracewa taba kundin tsarin mulkin da gwamnatin ta yi biris da shi