1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Tahoua ta kasar Nijar

Salissou Boukari
November 2, 2016

Mutane 20 ne suka rasu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin Makiyaya da Manoma a kusa da garin Bangui cikin gundumar Madaoua a jihar Tahoua.

https://p.dw.com/p/2S21a
Frauen mit Ziegen in Zentral-Niger (Zinder)
Hoto: DW/Larwana Hami

Da yammacin ranar Talata dai ofishin ministan cikin gidan kasar ta Nijar ya sanar da adadin mutane 18 da suka mutu yayin da wasu 43 da suka samu raunuka sannan aka yi kone-konen gidaje da dama. Sai dai kuma ya zuwa wayewar wannan rana ta Laraba, adadin ya kai na mutune 20 da suka mutu.

Tuni dai gwamnati ta aike da jami'an tsaro a yankin, inda kawo yanzu kura ta lafa, kuma jami'an tsaron na ci gaba da yin larwai domin kare lafiyar al'umma da dukiyoyinsu. Tun a ranar Talata da rikicin ya auku, minista cikin gidan kasar ta Nijar Bazoum Mohamed, ya yi kira ga dukannin bangarorin da ma sauran al'ummar kasar da su zuba wa zukatansu ruwa tare da kauce wa duk wasu abubuwa da za su kai ga samun irin wannan matsalar ta kashe-kashe da ke haddasa babban koma baya a kasa, tare kuma da shan alwashin zakulo duk wadanda ke da hannu cikin wannan lamari domin ganin sun gurfana a gaban shari'a.