1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Daidaita aikin yada labarai

Isuhu Mammane/ASDecember 29, 2015

Hukumar CSC da ke kula da tace labarai a Jamhuriyar Nijar ta girka cibiyoyinta a sauran sassan kasar don daidaita lamura.

https://p.dw.com/p/1HVeP
Burundi Bujumbura Pressekonferenz Journalisten
Hoto: DW/J. Johannsen

Wannan matakin da hukumar ta dauka dai wani yunkuri na ganin lamura da suka danganci watsa labarai a kasar na tafiya kamar yadda ya dace musamman ma dai da ya ke kasar na gab da gudanar da zaben shugaban kasa. Wannan yunkuri dai ya kawo karshen aikin da jami'an tsaro sau tari kan yi na sanya ido kan aikin jarida a kasar.

'Yan jarida a Nijar din dai sun jima suna mafarkin ganin wannan kungiya ta fadada aikinta zuwa sassan kasar maimakon birnin Yamai inda nan ne kawai ta fi karfi. Wani dan jarida mai suna Idrissa Adamou da ke jagorantar gidan rediyon Sarauniya mai zaman kansa ya ce ''manema labarai za su bawa hukumar ta CSC hadin aki wajen gudanar da aikinta amma kada ya kasance ta sanya son zuciya a wajen aikinta.''

Guinea Conakry Wahlen Cellou Dalein Diallo
Hoto: Reuters/L. Gnago

Hukumar CSC din ta bakin wani babban jami'inta Musa Muhammadu ya ce za su aiki kamar yadda doka ta tanada don ganin aikin jarida a kasar ya tafi bisa ka'ida. Shi kuwa Muhammadou Mamouda ya ce za su yi amfani da kayan aikinsu da nufin daukar matakan ladabtarwa ga wanda suka saba ka'idar da aka rigaya aka gidaya.

Angola Medien Prozess Aktivisten in Luanda
Hoto: DW/P.B. Ndomba

Tuni da 'yan jarida a Nijar din suka fara tofa albarkacin bakunansu kan wannan batu inda suka shawarci hukumar da ta yi aiki bil hakki da gaskiya kana ta kauracewa amfani da karfin da ta ke da shi wajen yi wa manema labarai bita da kulli yayin da suke gudanar da aiyyukansu.