1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kawancen jam'iyyu ya fara rikidewa

Abdoulaye Mamane AmadouFebruary 29, 2016

An nuna damuwa da yadda ake amfani da wasu manufofi da ba su dace ba wajen nenam kulla kawancen jam'iyyu.

https://p.dw.com/p/1I4ST
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar a yayin da hankali ya karkata izuwa ga zawarcin jam'iyyun siyasa da na 'yan takara wani abin da ya fara ci wa 'yan rajin kare hakin demukradiyya da ma wasu 'yan siyasar kasar tuwo a kwarya shi ne amfani da wasu manufofi na rabin kai ko na cimma wata moriya wajan kulla kawance maimakon akida ko nuna kishin kasa.

A lokacin da yake bayyana ra'ayinsa Malam Nouhou Arzika wani dan fafatukar rajin kare demukradiyya kuma jagoran wasu kungiyoyin farar hula da ke fafatukar inganta demukradiyya da fafatukar kare hakin dan Adam a kasar ta Nijar ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda batun kulla kawance a kasar ke neman rikidewa ya karkata zuwa cimma wasu manufofi na radin kai ko burin cimma wata gajiya. Ya ce hakan na da hatsari domin ba a la'akari da akidojin kishin kasa da ek ci gaba da samun gindin zama.

Dan rajin kare demukraduiyyar ya ce abubuwan da ke faruwa yanzu abin tsoro ne kana dokokin kasar sun hana.

"An gama kai da su don a yaudari al'umma. Idan ka duba fagen siyara yanzu dukka an gama kowa da kowa ba wata akida. Akwai da dama wanda yanzu haka sun shiga har siyasa ce don ta kasance wata 'yar kusa. Watom ana so a mayar da ita wata harka ta kashe muraba, wadda kuma doka ta hana ta."

Kawance don kishin kasa ba neman romon duniya ba

Dan takarar baya bayan nan da ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takarar jam'iyar PNDS Tarayya shi ne tsohon Firaminista Cheiffou Amadou.

Niger Kommunikationsminister Yahouza Sadissou Madobi
Yahouza Sadissou Madobi, kakakin RSD GaskiyaHoto: DW/D. Köpp

To sai dai kakakin jam'iyyar RSD Gaskiya Yahouza Sadissou Madobi ya musanta garzayawar da dan takarar na su yayi da ta'allaka ta da neman abin duniya.

"Can ma tare muke ba rabuwa muka yi ba, dukkan matsalolin da aka fuskanta mun gyarasu don gyara ka tafi da wanda ka saba fiye da wanda ba ka sani ba. Saboda haka in sha Allah za mu yi shekaru biyar a nan gaba don cimma manufofinmu da burin da shugaban kasa ya saka a gaba."

An lashi takobin yaki da akidar nuna banbanci

Daman dai tun kafin a kawo wannan matsayin fagen na siyasar Nijar burkuce yake da wasu kalamai da wasu 'yan siyasar ke amfani da su na nuna jihanci da ma banbancin kabila domin nuna fifiko a tsakanin wani dan takara izuwa wani dantakara, abubuwan da wasu 'yan siyasar kasar suka ce a yanzu za su tashi haikan domin kalubalantarsa.

Niger Präsidentschaftswahl Ergebnisse
'Yan Nijar sun zura ido su ga yadda za ta kayaHoto: DW/K. Gänsler

Malam Soumaila Amadou shugaban jam'iyyar Awaiwaya ne da ke jamhuriyar Nijar.

"Maganar ka sake ai ba maganar mutun daya ko biyu ba. Idan ka dauki Mahamadou Issoufou ai jam'iyyar tarayya ne ai ba kasa aka ce ba. Shi kuwa Hama Amadou, Lumana aka ce ai ba kasa ba aka ce ba. Saboda hakan mu maganar kasa muke amma wadanga 'yan korensu su suke neman su saka mu inda ba za mu samu sanin shiga ba, su ne za mu yaka mu hanasu domin kada su barmu cikin matsala: Su bar mana kasarmu mu kwana lafiya, mu tashi lafiya."


Kundin tsarin mulkin jamhuriyar ta Nijar dai yayi tir da Allah wadarai da nuna halaiya makamantan kabilanci ko jihanci da banbancin jinsi. Kana dokokin kasar na shari'a sun tanadi hukunci mai tsanani ga wanda duk ya fifo fili ya nuna haka.