1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kiran shiga yajin aiki bai samu karbuwa ba

Mahaman Kanta/ MNAApril 28, 2016

Kungiyoyin farar hula da na kwadago sun bukaci jama'a da su shiga yajin aiki saboda karan tsaye da hukumomi ke yi wa tsarin demokradiyya.

https://p.dw.com/p/1Ievj
Niger Citoyen Markt Boykott in Niamey
Hoto: DW/M. Kanta

Shugabannin kungiyoyin fararen hula da na 'yan kwadago a Nijar sun nemi masu sana'a da su kaurace wa wuraren sana'o'insu don nuna rashin jin dadinsu game da rashin aiwatar da demokradiyya kamar yadda ya dace a kasar wanda gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou ke yi.

Wakilinmu na Yamai Mahaman Kanta ya ce kungiyoyin sun ambata hakan ne a wani taron manema labarai da suka kira. Mahamadou Gamatie shi ne shugaban hadin gwiwar kungiyoyin direbobin Taxi da ke cikin hadaddiyar kungiyar da ta yi wannan kiran wato Résistance Citoyen ya yi karin bayani.

"Demokradiyya a Nijar a wannan lokacin babu ita. An mayar da doka gefe, magabata suna abin da suka ga dama ba tare da sun yi aiki da kundin tsarin mulki da dokokin kasa ba. Kasa kuwa in babu demokradiyya to akwai matsala. Talaka ba zai ci moriyar demokradiyya ba idan magabata na yi wa dokokin kasa karan tsaye."

Rashin biyayya ga bukatar rufe wuraren sana'a

To sai dai duk da wannan kira da 'yan kwadagon suka yi, 'yan kasuwa a babbar kasuwar da ke birnin Yamai sun cigaba da kasuwancinsu. Abin da ke nuna cewa kiran ba samu karbuwa ba kwata-kwata.

Niger Citoyen Markt Boykott in Niamey
An bude shaguna a babbar kasuwar birnin YamaiHoto: DW/M. Kanta

'Yan kasuwar da ba su yi biyayya da wannan kira ba, sun ce rashin samun cikakken biyani daga kungiyoyin farar hula ya janyo haka, kamar yadda wani dan kasuwa da ake kira Salissou Mahamane ya nunar.

"Matsalar da ke akwai shi ne mafi yawan kungiyoyin farar hula a Nijar ba sa cudanya da jama'a. Ya kamata su fadakar da mutane, kuma fadakarwa ta kut da kut."

Amma a bangaren wadanda suka yi wa wannan kira biyayya a babbar kasuwar birnin Yamai kamar irinsu Adamou Tahirou ya ce an bude kasuwa amma mutane ba su zo ba.

"Abin da ya sa saboda "Ville Morte" ne kuma mun bi bayan "Ville Morte" wato gurgunta hada-hada gaba daya. Mu dai ba mu buda ba. Wadanda suka buda 'yan kalilan ne, wadanda ba su buda ba sun fi yawa."

A ranar Lahadi dai an haramta wa kungiyoyin farar hula gudanar da wata zanga-zangar lumana da suka shirya yi. Sai dai har yanzu sun ce suna kan bakansu, kuma a ranar Asabar za su gudanar da zanga-zanga da jerin gwanon domin jan hankalin hukumomi su tabbatar da bin demokardiyya a kasa.