1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sakin talala ga wadanda ake zargi da juyin mulki

Salissou Boukari
March 25, 2017

Wata kotu a birnin Niamey ta sallami wasu fararen hulla akalla 10 galibinsu 'yan siyasa da kuma wasu jami'an Custum da aka tsare fiye da shekara guda bisa zargi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar NIjar.

https://p.dw.com/p/2ZwMA
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Harabar Kotun birnin YamaiHoto: DW/M. Kanta

 Alkali mai bincike ya yi wa wadannan mutane sakin talala bayan da ya nazarin laifukan da ake zarginsu da aikatawa. Wakilinmu na birnin Yamai Abdoulaye Mamane Amadou ya tattauna da Maitre Ali Kadri lawyan da ke kare wasu daga cikin 'yan siyasar da aka zarga da juyin mulkin, wanda ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce cikin 'yan farar hullan akwai 'yan majalisa biyu.

Sannan lawyan ya ce sakin na talala ne kafin a je ga shari'a ko ma da y ke ya ce bai san lokaci da za a je ga wannan shari'a ba.
Tun dai a ranar 17 ga watan Disamban na 2015 ne a wani jawabin da ya yi albarkacin bukukuwan zagayowar cikar shekaru 57 da samun mulkin kan kasar ta Nijar, Shugaba Issoufou Mahamadou ya sanar da cewa wasu gungun mutane sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsa.