1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Shirin cire rigar kariyar wasu manyan jami'ai

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2017

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da kwamitin da zai duba batun cire rigar kariya ga wasu tsaffin ministoci biyu da kuma dan majalisa daya domin kotu ta sauraresu bisa zargin da ake yi musu.

https://p.dw.com/p/2ZLcJ
Sitzung des Parlaments in Niger
'yan majalisar dokokin Nijar sun kafa kwamitiHoto: DW/M. Kanta


Rahotanni daga majalisar dokokin kasar sun ambaci sunayen mutane uku, kamar su Honorable Sidi Lamine dan majalisar dokoki na jam'iyyar mai mulki ta PNDS Tarayya da ake zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, sannan akwai Malam Laouali Chaibou tsohon ministan kwadago kuma memba a jam'iyyar ta PNDS Tarayya da ake tuhuma da aikata ba daidaiba wajen daukan ma'aiakata aikin gwamnati, sai kuma wani da ya yi minista a shekara ta 2009 mai suna Ousman Galadima na jam'iyyar RSD Gaskiya mai da ke kawancen masu mulki da shima ake tuhumar shi da karkata guraben zuwa karo ilimi da wata kasar ta bai wa jam'huriyar Nijar.

Sitzung der Nationalversammlung in Niamey Niger
Zauran majalisar dokokin NijarHoto: DW

'Yan adawa da masu rinjaye na cikin kwamitin

Kwamitin dai ya kumshi wasu kananan kwamitoci guda uku masu membobi 15 ko wannensu daga bangaren jam'iyyu daban-daban da suka hada da na adawa da masu rinjaye. Honorable Saadou Dille shi ne shugaban rukunin 'yan majalisar dokoki na PNDS Tarayya mai mulki kuma daya daga cikin membobin kwamitin ya ce a yanzu da yake an kafa kwamitin za su shafe tsawon sati biyu suna aiki kuma da yardar allah ba a boye za su yi aikin ba.

Ko da yake har yanzu kwamitocin ba su kai ga soma aiki gadan-gadan ba don binciken laifufukan da kotu ke tuhumar tsoffin shuwagabannin da aikatawa ba, ka'idodin majalisar dai sun ce tilas ne sai 'yan majalisar sun gudanar da na su bincike kafin su kai ga amincewa ko akasin haka ga bukatar ta bangaran shari'a. Honorable Mourtala Alhaji Mamouda dan majalisar dokoki a karkashin jam'iyyar MNSD Nasara kuma memba a sabon kwamitin,  ya ce ya cancanta ne daga irin laifin da mutun ya yi, kamar idan laifi ne na an kama mutun hannu dumu-dumu ga ta'addanci, ko kuma laifi na siyasa dukanin wadannan abubuwan dole sai an yi su cikin tsanaki ba tare da garage ba.

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Majalisar dokokin jamhuriyar NijarHoto: DW

Sai 'yan majalisar sun yi kwararan bincike

Kundin tsarin gudanar da harkokin majalisar dokoki a ayarsa ta 51, ya kuma tilasta wa kwamitocin sauraren wadanda a ke tuhuma don su bayar da ba'asi kafin majalisar ta kai ga amincewa da bukatar, wannan lamarin na zuwa ne a ya yin da ake takon saka tsakanin bangaren da ke mulki da na 'yan adawa bisa kakkame kusoshin jam'iyyunsu kan dalilan gwamnati na yaki da cin hanci da rashuwa.