1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta yi ikrarin samun nasara kan Boko Haram

Gazali Abdou tasawaJanuary 5, 2016

Shugaban hafsan sojojin Nijar Janar Seini Garba ne ya bayyana hakan a wannan Talata a gidan radiyon gwamnatin kasar dabra da bikin barka da shiga sabuwar shekara ga Shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1HYx7
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

A jamhuriyar Nijar shugaban hafsan sojojin kasar Janar Seini Garba ya ce sannu a hankali dakaran sojin kasar na kara samun nasara kan mayakan Kungiyar Boko Haram wacce ke ta faman kaddamar da hare-haren a yankunan kan iyakar Kudu maso Gabashin kasar.

Shugaban Hafsan sojin kasar ta Nijar ya bayyana hakan ne a wannan Talata a gidan radiyon gwamnatin kasar dabra da bikin gabatar da barka da shiga sabuwar shekara da ya gudana a fadar shugaban aksar ta Nijar a wannan rana ta yau.

Janar Seini Garba ya kara da cewa koma da yake har yanzu Kungiyar na da sauran karfin halin kaddamar da hari amma a zahiri ta ke cewa sun yi mata lahani sosai kuma suna samun nasara a kanta inda ta kai matsayin da ba a yau ba ta iya tunkarar sojin kasar ta Nijar gaba da gaba a fagen daga.

Duk da ya ke dai bai bada wasu cikakken bayanai na irin nasarorin da sojin kasar ta Nijar suka samu kan Kungiyar ta Boko haram ba, ya bayyana fatan za su samu damar ida murkushe ta a cikin wannan shekara ta 2016.

Daga farkon watan febrarun zuwa 18 ga watan Desemba na shekarar da ta gabata Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare 74 a yankin Kudu maso Gabashin kasar na kan iyaka da Tarayyar Najeriya.