1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Watsi da tayin shiga gwamnatin hadin kan kasa

Abdoulaye Mamane Amadou/ MNAAugust 4, 2016

Wannan ba shi ne karon farko da shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya gayyaci 'yan adawa da su shiga cikin gwamnati don gina kasa ba.

https://p.dw.com/p/1Jbm3
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

A jawabinsa ga 'yan kasa albarkacin bukukuwan shekaru 56 na samun 'yancin kai shugaban Nijar Issofou Mahamadou cewa yayi:

"Har yanzu ina da yakinin cewar hadin kan 'yan Nijar ne kawai zai iya sa mu kalubalanci matsalolin da muke fuskanta musamman ma na tsaro da ke addabarmu. Saboda haka ina sake mika hannuna ga kowa don fatan samun goyon baya."

Shugaban kasar na kalaman ne bisa fatan ganin ya kafa wata gwamnatin hadin kan kasa da ke kumshe da 'yan adawa don tunkarar muhimman matsaloli da ke addabar kasar ta Nijar.

Kokarin raba kan 'yan kasa

Sai dai tuni 'yan adawa suka yi fatali da tayin shugaban suna masu cewar a kai kasuwa duba da halin matsi da rashin iya jagoranci da suka zargi shugaban da aikatawa. Injiniya Rabilou Alhaji Kane kakakin jam'iyyar MNSD Nassara ne mai adawa.

Seini Oumarou Niger
Seini Oumarou shugaban jam'iyyar adawa ta MNSDHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ya ce: "Wanda ke da kashi kusan 93 cikin 100 na 'yan kasa da ke bayan shi mu in mun zo me za mu iya yi, kuma yaya za ya yi wannan kiranmu, idan muka zo akwai abinda za mu karawa? Ya je ya yi aiki da kashi 93 na 'yan kasar da ke tare da shi da ke bayan shi. Su kadai sun isa su kawo mai sauyi. Idan ya yi niyya ai niyya ce, mu a bangaren MNSD Nassara wannan kiran sai dai mu ce a je a kai kasuwa. Idan ma mun je mu jam'iyyun adawa mi za mu iya yi mashi?"

A nata bangare ita ma jam'iyyar Lumana Afrika ta tsohon kakakin majalisar dokoki Hama Amadou cewa ta yi kiran na shugaban wani sabon salo ne kurum na kara rarraba kawunan jam'iyyun siyasa, kamar yadda Alhaji Salissou Mahamane Leger kakakin Jam'iyyar ta Lumana Afrika ya nunar.

Ya ce: "Idan ka dauki wancan lokacin da aka yi gwamnati ta hadin kan kasa ya raba kanun 'yan kasa ko kuwa hadin kansu aka yi? Ta kaka mutum yana da kashi 92.72 cikin 100 a ce yana bukatar kashi din nan 7 kawai cikin 100 don gina kasa? Don haka kawai wani salo ne yalla idan ma har 'yan siyasar nan gaba daya na adawa suka bishi barnar da aka yi da abubuwan da aka yi da yadda ake jagorancin kasar nan babu abin da zai iya canzawa."

Hama Amadou
Hama Amadou shugaban jam'iyyar Lumana AfrikaHoto: DW/S. Boukari

Gwamnati za ta ci-gaba da aikinta

To ko yaya jam'iyyar PNDS Tarayya ta ji da watsi da wannan tayin da 'yan adawa suka yi? Ga abinda kakakin jam'iyyar Assoumana Mouhamadou yake cewa.
"Idan 'yan adawa sun ki amincewa da su shiga cikin gwamnati to gwamnati za ta ci-gaba da aiki tun da babu wata gardama da muke da a majalisa da yardar Allah."

A zaben shugaban kasar da ya gabata dai na 20 ga watan Maris da 'yan adawa suka kauracewa ya bai wa Shugaba Issoufou damar darewa a kan madafan iko da sama da kashi 92 cikin 100 tare da tallafin wasu kawancen jam'iyyu 53. Sai dai duk da hakan shugaban ya kara nanata wannan kiran don kafa gwamnatin ta hadin kan kasa kamar yadda aka yi a ranar 13 ga watan Agustan shekarar 2013, duk ko da cewa kafata ya haifar da tarnaki da yawa a fagen siyasar kasar.