1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Zargin murde sakamakon zaben shugaban kasa

Mahamane Kanta/ASFebruary 23, 2016

Al'ummar Nijar na cigaba da dakon sakamakon zaben gama-gari, 'yan adawa na zargin jam'iyya mai mulki da kokarin murde sakamakon zabe.

https://p.dw.com/p/1I0S5
Niger Wahl Wählerin in Niamey
Hoto: DW/M. Kanta

Yayin da ake jiran sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, 'yan adawa na cewar jam'iyya mai mulki na kokarin amfani da karfin iko wajen murde sakamakon zabe. Shugaban jam'iyyar UDR Tabbat ya ce sakamakon da CENI ke badawa ya sha banban da abinda ya ake da shi a mazabun da aka kada kuri'a.

A wani taron manema labarai da suka yi, 'yan adawar suka ce a halin da ake ciki ba za su yi amince da sakamakon da CENI din ke fiddawa ba. Wannan takaddama da ta kunno kai dai na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da tattara sakamakon zaben na ranar Lahadi wanda al'ummar kasar suka kagu su ji cikakken sakamakon don sanin wanda zai jagoranci kasar a wani sabon wa'adi na shekaru biyar.

Tuni dai hukumar CENI din da ke da alhakin shirya zabe da ma bayyana sakamakonsa ta nesanta kanta daga wannan zargi da ake mata na hada hannu da masu mulki wajen murde sakamakon zabe. A share guda kuma hukumar ta ce ta na cigaba da tattara sakamakon zaben a babbar cibiyar tattara sakamakon wadda ke babban dakin taron nan na Palais Des Congres da ke babban birnin kasar Yamai.