1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:Jam'iyyar MNRD ta raba gari da MNSD

March 28, 2017

Jam'iyyar MNRD Hankuri ta tsohon shugaban Nijar Mahaman Ousman kana tsohon kakakin majalisar dokoki wacce ke da wakilai a majalisar dokoki a yanzu ta daina yin kawance da jam'iyyar MNSD Nasara.

https://p.dw.com/p/2a91Z
Plakat Ousmane
Hoto: DW/M. Kanta

Jam'iyyar ta MNRD Hankuri da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahamane Ousmane wanda ya yi takara da ita a zabubukan da suka gabata na watan a shekara ta 2016 na a matsayin babbar jam'iyyar da ke dasawa da jam'iyyar Mnsd nassara wacce shugabanninta ta hanyar wani dadden kawance suka mulki Jamhuriyar Nijar har na tsawon shekaru da dama.Amma a yanzu sun raba gari saboda MNSD Nasara ta bi bayan gwamnatin.

Wannan lamari dai da ya faru na ficewar 'yan majalisun na MNRD daga kawance da suke yi da MNSD a majalisar zai iya kara wa 'yan adawar karfi musammun ma jam'iyyar Modem Lumana ta Hama Amadou.Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ake samun canje-canje na jam'iyyun siyasa a Nijar ba.