1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:'Yan adawa na bukatar a kira taron CNDP

Abdoulaye Mamane Amadou/GATAugust 7, 2015

'Yan adawar kasar ta Nijar sun bukaci gwamnati da ta kira taron hukumar sasanta rigingimun siyasa ta CNDP domin samun fahimtar juna akan batutuwa da dama kafin shiga zabukan shekara ta 2016

https://p.dw.com/p/1GBqv
Hajiya Hauwa Abdu
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Rikicin baya bayan nan da ya kara tsamin dangantakar da ta jima dama da gurbacewa tsakanin bangarorin siyasar kasar ya samo asali ne tun daga ranar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta bayar da jadawalin zabe wanda 'yan adawa suka ce ta yi shishigi da wuce gona da iri dangane da hurumin da doka ta ba ta, da kuma matakin cire rigar kariyar wasu 'yan adawar da ake tuhuma da aikata wani laifi, cikinsu har da tsohon Shugaban Kasa Mahamane Ousmane.Kuma wadannan na daga cikin manyan dalilai da kawancen adawar na ARDR ya yi amfani da su domin kiran gwamnati da ta gagauta kiran taron hukumar sasanta rigingimun siyasa ta CNDP.
Honnorable Tidjani Abdoulkadri sakataren jamiyyar MNSD ne mai adawa.

Dalillan 'yan adawar Nijar na neman kiran taron CNDP


" Yanda muke ganin abubuwan na tafiya tun daga rijistan masu zabe zuwa bayyana jadawalin tsarin zabuka ne muka gano akwai matsaloli. Na biyu mun san da cewar idan har aka ce zabe to dole sai ka ce jamiyyun siyasa kenan, to mun lura da cewa gwamnati na amfani da wannan damar, tana watse jamiyyunmu kuma tana baiwa wasu daga cikinmu tsoro ta hanyar wasu salo na haramta wa wasu tsayawa takara ko a gaba, hakan kuma idan har muka yi shuru ba mu maganta akan batun ba, To kwa muna ganin zai wuya a samu zabuka masu haske".

Tijani Abdulkadiri
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Tuni dai bangaren na adawa ya ce ya aike da wasika zuwa fadar Firaministan kasar kuma yanzu ya na jiran kira daga fadar domin tsayar da taron.
To amma sai dai a ganin Alhaji Sanoussi Tambari Jackou Babban mashawarci na musamman a fadar shugaban kasa kuma shugaban jamiyyar PNA Alumma, kan batun na jadawalin zaben dai 'yan adawar sai dai su rungumi kaddara

Matsayin bangaren masu milki kan bukatar 'yan adawa

" Shi taron na CNDP ba ya da izini ba ya da hujja ko daya kan abinda hukumar zabe ta tanada, ko da 'yan iya kawo fitina ta siyasa, idan har ya na kawo fitina hukumar zabe ta lura da hakan sai a bata shawara ta lura idan ta ga dama ta karba ta sake shi ,amma wani ba ya iya ce mata dole ta sake, taron CNDP ba ya iya ce mata komi" .

Ko mi take ciki dai halin da ake neman shiga a yanzu na da bukatar zama domin yi masa karatun ta nutsu da dubin juna cikin idon rahama saboda kauce wa shiga cikin wani yanayi na rashin tabbas in ji Honnorable Tidjani Abdoulkadri sakataren jamiyyar ta Mnsd mai adawa.

"Akwai matsala CDS, akwai matsala LUMANA, akwai matsala a MNSD saboda hakan mu ke ta wadannan maganganun. Ya kamata kenan a gyarasu da gaggawa don ba za mu yarda ba a ce a yi ta jan mutane a cikin wani rudani na sharia har a kai wani lokaci da wasu za su ce wai wane ko wane ba za su tsaya takara ba mu wannan ba za mu yarda da shi ba.

Sai dai, a cewar Alhaji Sanoussi Tambari Jackou Shugaban Jamiyyar PNA Alumma na gungun kawncen masu rinjaye batun ba haka yake ba.

" Wannan batun cece-kucen banza ne na tsegumin siyasa da ake yi, siyasa ce kawai irin wannan abin na a sabto nan a sabto can kowa ma yana yin shi. Shin wai mine ne da mutane sun yi laifi an ce ana shirin tube masu rigar kariya ko an cire masu, sai a yi ta burususwa a yi ta dumi kamar wani tashin dunya".

Niger Mohamed Bazoum Porträt
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanzu dai hankali ya karkakata kan zaman taron hukumar ta CNDP domin jin irin shawarwarin da za su fito daga dakin taron da masharhanta ke ganin da kyar taron ya gudana a cikin laluma, ganin tsananin takun sakar da ke gudana a tsakanin jamiyyun na adawa da na masu rinjaye

------------------------------
Abdoulaye Mamane Amadou DW/Hausa daga Niamey Niger