1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nkurunziza ya lashe zaben Burundi

GazaliJuly 24, 2015

A Burundi shugaba Pierre Nkurunziza ya yi nasarar yin tazarce bayan da ya lashe sakamakon zaben shugaban kasa, kamar yadda hukumar zabe ta sanar ranar Jumma'a.

https://p.dw.com/p/1G4O2
Burundi Präsident Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre NkurunzizaHoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

A Burundi shugaba Pierre Nkurunziza ya yi nasarar yin tazrce bayan da ya lashe sakamakon zaben shugaban kasa da kashi 69,41 daga cikin dari na kuri'un da aka kada.Hukumar zaben kasar ce ta bayyana haka lokacin wani taron manema labarai da ta kira a yammacin yau a birnin Bujumbura inda ta bayyana sakamakon wucan gadi na zaben.Tuni kuma bangarorin yan siyasa na aksar ta Burundi suka soma tofa albarkacin bakinsu kan sakamaon.Gazali Abdu Tasawa ya hada mana wannan rahoto.

Sakamakon wucan gadi da shugaban hukumar zaben kasar ta Burundi Pierre Claver Ndayicariye ya bayyana a yammacin wannan Juma'a ya nunar da cewa tun a zagayen farko Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi nasarar yin tazarce kan kujerar milkin kasar ta Burundi bayanda ya samu kashi 69;41 daga cikin dari na kuri'un da aka kada,inda ya lashe jihohi 16 daga Cikin 18 daga ciki har da babban birnin kasar Bujumbura inda zanga-zangar nuna adawa da shi ta fi kamari. Abokin hamayyarsa Rwasa Agathon ya tashi da kashi 18,99. Sai dai tuni ya nuna shakkunsa a game da sahihancin wadannan alkalumma yana mai cewa.

"Ya ce duk abunda suka bayyana ba gaskiya ba ne ,aringizon kuri'u ne suka yi domin sun sha kayi"

Sai dai madugun 'yan adawar kasar ta Burundi na mai ra'ayin ganin an dakatar da duk wani rikici a kasar domin sake komawa a kan tebirin tattaunawa.

"Ya ce ba wai na amince ba ne da sake zaben Pierre Nkurunziza, amma dai ina ganin tsakanin matsaloli biyu ya kamata mu dauki maras tsanani.Ma'ana maimakon kowa ya yi tsayuwar gwamin jaki akan matsayinsa kamata ya yi mu kama shawarar da kasashen duniya suka jima suna ba mu ta hawa tebirin tattaunawa domin shawo kan matsalar cikin ruwan sanhi, ina ganin hakan zai fi zama alkhairi.

To sai dai a daidai lokacin da madugun yan adawar ke ganin ya kamata bangarorin da ke hamaya da juna su koma tebirin tattaunawa,wani bangaran jam'iyyun adawar kasar ya yi watsi da sakamakon tare da yin kira da a zare dantse domin ci gaba da kalublantar shugaban kasar da gwamnatinsa.

"Ya ce mu mun dauka cewa ba zabe ba ne aka yi rufa-rufa ce kawai aka yi .Dan haka mu ba za mu taba amincewa da sakamakon zaben ba sannan ba za mu mutunta duk hukumomin da za a girka ta hanyar sakamakon wannan zabe ba hasalima za mu ci gaba da yakarsu."

A daidai lokacin da a bangaran 'yan adawa ake wadannan korafe korafe da soma bulluwar sabanin ra'ayi a tsakaninsu , daga bangaran jam'iyyar CNDD-FDD ta Shugaba Pierre Nkurunziza dai cewa ake Allah san barka da wannan sakamako wanda zabi ne na yan kasa. Ndabirabe na daga cikin magoya bayan wannan jam'iyya dama Shugaba Pierre Nkurunziza.

Afrika Wahl in Burundi
Kada kuri'a a zaben BurundiHoto: Reuters/M. Hutchings

"Ya ce al'umma ce ta kaishi a nan inda ya ke kuma ita ce ta sake zaben shi da gagarimin rinjaye,dan haka ko ana so ko ba a so N'kurunziza mutuman yan kasa ne"

Ko ma dai mi ake ciki sakamakon wannan zabe ya baiwa Shugaba Pierre Nkurunziza wanda ke kan shugabancin kasar tun a shekara ta 2005 damar cika gurinsa na sake ci gaba da milkin nasa a wani wa'adi na ukku, wannan kwa duk da irin adawar da shirin nasa ya fuskanta daga bangaran 'yan siysa da kungiyoyin farar hula na kasar dama manyan kasashen duniya. Abun jira a gani a nan gaba shi ne matakin da masu adawa da wannan zabe na shugaba Pierre Nkurunziza a ciki dama wajan kasar za su dauka domin kalubalantar milkin tazarcen nasa. A nan gaba ne dai Kotun Kolin kasar za ta bayyana kammalallen sakamakon zaben wanda zai tabbatar da sabon wa'adin milkin shugaban a hakumance.