1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NLC da TUC na tattaunawa da gwamnatin Najeriya

Salissou BoukariMay 17, 2016

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soma ganawa da kungiyoyin kwadagon kasar a wani mataki na samun mafita kan yunkurinsu na zuwa yajin aikin gama gari.

https://p.dw.com/p/1Iouq
Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoto: dapd

Har dai ya zuwa yammacin ranar Litinin kungiyoyin kwadagon kasar biyu da suka hada da Nigeria Labour Congress (NLC), da kuma Trade Union Congress (TUC), na wata tattaunawa ta keke da keke da gwamnati domin samun mafita. Sai dai a cewar Achese Igwe na kungiyoyin mai na Nupeng da Pengassan ya ce su dai ko mi take ciki ba za su shiga wanan yajin aiki ba, inda ya ce suna goyon bayan matakin da gwamnatin ta dauka wadda ita ce hanya ta bunkasa tattalin arzikin kasar.

Gwmnatin ta Najeriya dai ta cire tallafin kudin man ne domin kirkiro da wasu fannoni da za su samarwa da jama'a ayyukan yi a kasar inda yanzu farashin man a gijajen mai ya kai Naira 145.