1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nuri Al-Maliki ya yi jawabi a gaban majalisun dokokin Amirka

July 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bup4
FM Iraqi Nuri Al-Maliki ya yiwa zaman hadin guiwa na majalisun dokokin Amirka jawabi. Maliki ya jaddada cewa Iraqi na kan gaba a yakin da ake yi da ta´addanci kuma masu ta da kayar baya a kasar na aikata babban laifi ga addinin Musulunci. A lokuta da dama cikin jawabin nasa Maliki ya yi ta godewa Amirka da ta ´yanto Iraqi daga mulkin kama karya na Saddam Hussein. FM ya yi kira ga Amirka da kada ta yi watsi da kasar sa. Maliki ya yi kokarin dinke baraka da gwamnatin Washington bayan ya soki lamiri Isra´ila a rikicin da take yi da Hisbollah. A wani labarin kuma a yau aka sake gurfanad da tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein gaban kotu. Saddam ya fusata bisa cewa an tilasta masa zuwa kotun ne daga asibiti, inda ake yi masa magani sakamakon raunin da ya yi saboda yajin cin abinci da yake yi.