1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama-Ba zaman lafiya muddin masu kudi na danne talakawa

Yusuf BalaSeptember 20, 2016

Shugaban na Amirka ya ce zaman lafiya a duniya ya dogara a kokari na rage wagegen gibi da ke tsakanin talakawa da masu hannu da shuni.

https://p.dw.com/p/1K5Zt
UN Vollversammlung 24.09.2014 - Barack Obama
A cewar Shugaba Obama rage wagegen gibi tsakanin talaka da mai kudi shi zai kawo zaman lafiyaHoto: Getty Images/Spencer Platt

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana kalamai masu zafi a lokacin da yake jawabinsa da ke zama na karshe a matsayin shugaban Amirka gaban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya inda ya yi suka mai zafi ga kasar Rasha da ke mara baya ga mahunkuntan Siriya da shirin tsagaita wutarsu ya rushe da ma katsalandan din mahukuntan na birnin Moscow a Ukraine.

Shugaba Obama ya dai jaddada cewa samar da waraka a rikicin na Siriya mai yiwuwa ne kawai idan aka bi hanyoyi na diplomasiya.

Ya kuma juya kan batun zaman takewa a duniya inda ya nunar da cewa zaman lafiya a duniya ya dogara a kokari na rage wagegen gibi da ke tsakanin talakawa da masu hannu da shuni:

"Duniyar da ta kasance kashi daya cikin dari suke rike da arzikin al'umma ragowar kashi 99 ko oho ba za samu daidaito ba."